Masarautar Zazzau ta nada karin sabbin hakimai takwas tare da mika musu takardun fara aiki.
Mai Martaba Sarkin Zazzau, Malam Ahmed Nuhu Bamalli, ne ya kaddamar da sabbin hakiman a wani kwarya-kwaryan biki a fadarsa da ke birnin Zariya.
- INEC ta fitar da jerin rumfunan zabe 124 da ta soke
- NAJERIYA A YAU: “Kasuwanci Ya Mutu Idan Ana Kin Karbar Tsofaffin Kudi” – Dan Kasuwa
Sarkin Zazzau ya kuma mika wa sabbin hakiman takardunsu na aiki, wanda ya nuna nadin nasu sun fara aiki ne daga ranar 1 ga watan Fabrairu, 2023.
An nada su ne bayan amincewar Gwmanan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, ta hannun Ma’aikatar Kananan Hukumomi da Masarautu ta jihar.
Sabbin Hakiman su ne:
- Alhaji Sufiyanu Umar Usman, Karfen Dawakin Zazza, Hakiman Pambegua.
- Mohammed Dahiru Dikko, Barde Kankanan Zazzau – Hakimim Pala.
- Haruna Abubakar Bamalli, Barde Kerrariyyan Zazzau – Hakimin Zangon Aya.
- Alhaji Kabiru Zubairu, Madaucin Arewan Zazzau – Hakimim Barnawa
- Dokta Bello Lawal, Durumin Zazzau – Hakimim Gubuchi respectively.
- Abdulkarim Zailani – Hakimim Sabon Birni
- Alhaji Auwalu Aliyu Damau – Hakimim Samu
- Alhaji Aminu Mohammed Ashiru – HakiminHunkuyi.