Kotun ta tabbatar da nadin Alhaji Ahmad Nuhu Bamalli a matsayin Sarkin Zazzau na 19.
Babbar Kotun Jihar Kaduna da ke zamanta a Dogarawa, Sabon Garin Zariya ta yanke hukuncin ne a safiyar Juma’a, 6 ga Nuwamba, 2020.
- Yadda mutanen gari suka kare kansu daga harin ‘yan bindiga a Zamfara
- An sa ranar nadin sarautar sabon Sarkin Zazzau
- Uwa ta yi karar Mudassir & Brothers kan cin hakkin ’yarta da ta rasu
Alkalin kotun, Mai Shari’a, Kabir Dabo, ya kuma yanke hukunci cewa Gwamnan Jihar, Kaduna, Nasir El-Rufai na da ikon rantsar da Sarki Ahmad Bamalli da kuma ba shi sandar sarauta a ranar Litinin 9 ga watan na Nuwamba.
Kotun ta yanke hukuncin ne bayan karar da Iyan Zazzau, Alhaji Bashar Aminu, yana bukatar kotun ta ayyana shi a matsayin halastaccen Sarkin Zazzau ta kuma hana ba wa Sarki Bamalli sandar sarauta.
Bamalli na ikirarin cewa shi ne halastaccen wanda Masu Zabar Sarki na Masarautar Zazzau suka zaba da mafi yawan kuri’u don haka shi ya kamata a nada a matsayin sarki na 19.
Idan ba a manta ba, zaman kotun na baya, kotun ta ba da umarcin cewa kowanne daga cikin bangarorin ya tsaya a matsayinsa daidai yadda ake ciki a lokacin har sai ta yanke hukunmi.
Sarki Ahmadu Nuhu Bamalli daga gidan sarautar Mallawa, ya hau karagar mulki ne bayan rasuwar Sarkin Zazzau Alhaji Shehu Idris daga gidan Katsinawa, wanda Allah Ya yi wa cikawa a ranar Lahadi, 20 ga Satumba, 2020, bayan shekara 45 yana kan mulki.
Tun ranar 20 ga Satumba, 2020 Allah Ya yi wa Sarki na 18, Alhaji Shehu Idris rasuwa, sai dai ba a nada magajinsa ba sai bayan kwana 17.
A ranar Laraba 7 ga Satumba, 2020 Gwamnatin Jihar Kaduna ta sanar da nadin Sarki Ahmed Bamalli, wanda ta ce ya fara aiki nan take.
Bamali ya hau mulki ne bayan shekara 100 rabon gidan Katsinawa da yin sarautar Zazzau, tun bayan rasuwar kakansa, Sarkin Zazzau na 13, Alu Dan Sidi.
Kafin zamansa sarki, shi ne Magajin Garin Zazzau, rawanin da ya gada daga mahaifinsa, Alhaji Nuhu Bamalli.