A Karamar Sallar bana ce Sarkin Zazzau, Ahmad Nuhu Bamalli ya yi hawan farko bayan darewarsa a karagar mulkin Kasar Zazzau.
Hakimai 76 ne ke yin hawan a bukukuwan sallah daban-daban na kwanaki uku a kasar ta Zazzau.
- Yadda sauran masu sallar Tahajjud 10 da aka sace a Katsina suka kubuta
- Janar Dogonyaro: Buhari na alhinin mutuwar sojan da ya yi jawabin yi masa juyin mulki
Sarkin Zazzau ya nemi jama’arsa da ’yan Najeriya su kara dagewa wurin taimakon jami’an tsaro da rahotannnin domin bankado maboyan ’yan ta’adda da masu tada fitina a duk inda suke.
Sarkin ya bayyana haka cewa da haka ne kadai za a samu nasara a kokarin da gwamnati ke yi don yakar barazanar da ke damun al’umma.
Ya jaddada muhimmancin samar da ayyukan dogaro da kai ga matasa, saboda rage yawan ayyukan ta’addanci da wasu matasa ke shiga. Tare da sanya yara burin neman ilimin zamani da na addini.
Ahmed Bamalli ya bukaci manoma su kara himmatuwa a bangaren domin wadata kasa da abinci da wadatuwar tattalin arziki.
Ya jaddada muhimmancin ci gaba da aikin gayya tare da tsaftar muhalli domin rage wa gwamnati wani nauyi.
Sarkin na Zazzau ya nemi jama’a su ci rika bin matakan kariyar cutar COVID-19, tare da girmama umarnin likitoci da gwamnati saboda yanzu ana fuskantar barazanar cutar.
Sarkin Zazzau Ahmed Bamalli ya jinjina wa malamai saboda wa’azin zaman lafiya da addu’o’i da suka yi wa kasa a lokacin Tafsirin Ramadan.
Kuma ya yi fatan al’umma za su ci gaba da amfani da darussan da da Ramadan ya koyar domin samun tsira a duniya da gobe kiyama.