✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Sarkin Sasa ya nada wasu a sababbin sarautu

Sardaunan Yamma, kuma Sarkin Sasa Alhaji Haruna Maiyasin ya tabbatar da nadin wasu Hausawa biyar a matsayin mashawarta da za su taimaka wa fadarsa wajen …

Sardaunan Yamma, kuma Sarkin Sasa Alhaji Haruna Maiyasin ya tabbatar da nadin wasu Hausawa biyar a matsayin mashawarta da za su taimaka wa fadarsa wajen  gudanar da ayyukan wayar da kan jama’a a kan tsaron kasa da kyautata zamantakewa a tsakanin al’ummar Yarabawa da ’yan Arewa a sashin Kudu maso Yamma.

An gudanar da bikin mika takardun shaida ga mashawartan ne a fadar masarautar Hausawan Sasa da ke birnin Ibadan, Jihar Oyo, inda Sarkin da kansa ya mika satifiket ga Alhaji Balarabe Isa Surajo da aka nada masa rawani a matsayin Talban Yamma, a yayin da Sarkin Nufawan Ibadan, Alhaji Shehu Ibrahim, ya mika satifiket ga sabon Shantalin  Yamma Alhaji Isa Abdullahi. Sarkin Hausawan Idi-Araba da ke Legas, Alhaji Hassan Auyo, shi ne ya mika satifiket ga Alhaji Abdullahi Muhammed wanda aka nada a matsayin Sarkin Rafin Yamma, sai Sarkin Hausawan Ojoo Ibadan, Alhaji Ali Yaro, wanda ya mika satifiket ga Alhaji Ja’far Usman da aka nada a matsayin Tukuran Yamma a yayin da Marafan Ibadan, Alhaji Audu Lawal ya mika satifiket ga Alhaji Muhammed Sani Sulaiman wanda aka nada a matsayin Wakilin Unguwar Basorun a Ibadan.
Kafin a nada musu rawani da mika masu satifiket, sai da malamai suka karanto ayoyin Alkur’ani da Hadisan Annabi Muhammad (SAW) da ke tunatar da Musulmi a kan tsoron Allah da mu’amala da kyautata zamantakewa da jama’a da hakuri da gaskiya da rikon amana da yin adalci daga masu rike da shugabancin al’umma. A bangare daya kuma, masu kade-kade da busar algaita da maroka da mawaka ne suka nishadantar da mahalarta bikin.
Cikin jawabinsa, Sarkin Sasa, Alhaji Haruna Maiyasin, ya shaida wa mutanen da aka nada bisa wadannan sarautu cewa: “Sakamakon irin gudunmawar da kuke bayarwa ga jama’a wajen samar da ayyuka ga matasa ’yan Arewa da kuke zaune tare da su a wannan sashi da kyautata zamantakewarku da jama’ar gari, su ne suka kai ku ga wannan matsayi da muke fatan za ku kara jajircewa da sadaukar da kai wajen yin amfani da dukiyarku domin ci gaba da gudanar da irin wannan aiki. Kuma, ina so ku yi amfani da wannan dama wajen ilimantar da jama’arku su girmama dokokin mahukunta kuma ku bayar da kyawawan shawarwari a matsayin gudunmawarku ga ayyukan tsaron kasa da Shugaba Muhammadu Buhari yake yi.”
Da yake magana a madadin mutanen da aka nada, sabon Talban Jihar Yamma, Alhaji Balarabe Isa Surajo, ya fara da yin godiya ga Allah (SWT) ne da ya nuna masa wannan rana inda ya ce: “Ba zan taba mancewa da wannan rana ba kuma a madadin ’yan uwana, ina tabbatar da cewa, mun yi alkawarin yin aiki tsakani da Allah wajen ganin fadar Sarkin Sasa ta cimma burinta na samar da hadin kan mutanenmu da ci gabansu.”