Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar, ya yi wa wani matukin babur mai kafa uku sha tara ta arziki saboda mayar da kudin da aka manta a babur dinsa a Jos, Jihar Filato.
Aminiya ta rawaito cewa mutumin, mai suna Malam Akilu ya mayar da kudin da aka manta a babur din da yake haya a kwanakin baya.
- Akwai yuwuwar rabin ’yan Afghanistan su fuskanci yunwa – MDD
- Hisbah za ta tilasta masu son aure a Kano shiga makarantar koyon zamantakewa
Hakan dai ya sa Sarkin Musulmin ya bashi kyautar N500,000, kwatankwacin yawan kudin da aka manta a cikin babur din nasa, kan nagartar da rikon amanar da ya nuna.
Wakilin Sarkin Musulmi, Sarkin Wase kuma Shugaban Kungiyar Jama’atu Nasril Islam (JNI) a Jos, Alhaji Sambo Haruna, shi ne ya mika kyautar a lokacin taron kaddamar da sabbin shugabannin kungiyar a Babban Masallacin Jos.
Ya yaba da abin da mutumin ya yi, wanda ya ce ya dace da koyarwar Musulunci, da ake bukata daga kowane Musulmi.
“Mutane kar su manta cewa akwai sakamako ga kyawawan ayyuka. Muna alfahari da wannan matashi da ya yi abin yabawa da alfahari ga Musulmi da matasan a Jihar Filato.”
Sarkin Wase ya ce, “Bayan tabbatar da gaskiyar abin da ya faru, Sarkin Musulmi ta turo kwatankwacin kudin, N500,000 domin a ba wa Malam Akilu a matsayin kyauta.”
Da yake jawabi bayan ya karbi tukwicin, Malam Akilu ya ce, “Ina matukar farin cikin samun karramawa daga Sarkin Musulmi. Wannan wani abu ne da ban taba tsammani ba, ina addu’ar Allah Ya kara masa daukaka.”
Idan za a iya tunawa, ko a shekarar 2017 sai da Sarkin Musulmin ya bayar da irin wannan tukwicin ga wani direban babur din mai kafa uku mai suna Bashir Usman, wanda ya mayar da wata jaka mai dauke da kudi har kimanin N582,400, mallakin Mama Ijimah, wata ‘yar kasuwa Jos.