Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar ya bayyana Laraba, Yuli 19, 2023 a matsayin Muharram 1, 1445.
Tun ranar Litinin ne Sarkin ya umarci al’ummar Musulmi da su fara duban jinjirin watan Muharram na sabuwar shekarar Musulunci.
Watan Muharram shi ne watan farko bisa tsarin kalandar hijirar Annabi Muhammad Sallal Lahu Alaihi Wa Sallam daga Makka zuwa Madina.
An ba da hutun Sabuwar Shekarar Musulunci a Sakkwato
Sabuwar Shekarar Musulunci: Ganduje ya ayyana Litinin a matsayin ranar hutu a Kano
Kuma wata ne mai alfarma inda Musulmi kan yi azumin nafila na Tasu’a da Ashura ranar tara da 10 ga watan.
Sanarwar da Majalisar Sarkin Musulmi ta fitar ta ce “Sakamakon rashin ganin jinjirin wata a faɗin Najeriya, muna tabbatar da Laraba, Yuli 19, 2023 a matsayin ranar farko ta watan Muharram 1445H”.