✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

A fara duban watan Sabuwar Shekarar Musulunci —Sarkin Musulmi 

Za a shiga Sabuwar Shekarar Musulunci ta 1446 Bayan Hijira

Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Muhammad Sa’ad Abubakar ya umarci al’umma da su soma duban watan Muharram na Sabuwar Shekarar musulunci ta 1446 Hijiriyya daga ranar Jumu’a 5 ga watan Yuli, 2024.

A madadin Sarkin Musulmi, Wazirin Sakkwato kuma Shugaban Kwamitin Bayar da Shawara kan Harkokin Addini a Masarautar Sarkin Musulmi, Farfesa Sambo Wali Junaid, ne ya fitar da sanarwar.

Farfesa Sambo, ya ce duk wanda ya samu ganin watan ya sanar da Majalisar Sarkin Musulmi ko wani uban kasa ko hakimi domin sanar da al’umma.

Watan Muharram shi ne watan farko a tsarin watanni 12 na Shekarar musulunci.

Idan an ga watan, Asabar 6 ga watan Yuli, 2024, zai kasance ranar farko a shekarar 1446 Hijiriyya.