✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Sarkin Musulmi ya sanar da ganin watan Babbar Sallah a Najeriya

Hakan na nufin Alhamis ce daya ga wata

Mai alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar III ya tabbatar da ganin jinjirin watan Zul-Hijjah a Najeriya, wanda hakan ya tabbatar da ranar Alhamis a matsayin ranar daya ga watan.

Sarkin, wanda kuma shi ne Shugaban Majalisar Koli ta Harkokin Addinin Musulunci a Najeriya (NSCIA) ya ce ranar dai ita ce ta yi daidai da 30 ga watan Yunin 2022.

Hakan dai na nufin a bana za a yi bikin Sallah Babba ranar Asabar, tara ga watan Yulin 2022.

Watan Zul-Hijjah dai shi ne watan na 12 kuma na karshe a kalandar Musulunci, kuma a cikinshi ne Musulmai daga ko ina daga fadin duniya ke gudanar da Aikin Hajji a kasar Saudiyya.

Kazalika, yayin bikin Sallar, Musulmai kuma na gudanar da ibadar Layya, inda sukan yanka dabbobi domin raba naman ga ’yan uwa da mabukata.