✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Sarkin Musulmi ya ce a duba sabon watan Rabi’ul sani

Mai Alfarma Sarkin Musulmi Muhammad Sa’ad Abubakar ya umarci al’ummar Musulmi da su fara dubar jinjirin watan Rabi’ul sani 1442AH daga ranar Lahadi. Sarkin Musulmi…

Mai Alfarma Sarkin Musulmi Muhammad Sa’ad Abubakar ya umarci al’ummar Musulmi da su fara dubar jinjirin watan Rabi’ul sani 1442AH daga ranar Lahadi.

Sarkin Musulmi ya fitar da bayanin hakan ne ta hannun Shugaban Kwamitin Ganin Wata na Majalisar Sarkin Musulmi, Farfesa Sambo Junaidu.

“Ina sanar da al’ummar Musulmi su fara duba watan Rabi’ul Sani a gobe Lahadi daidai da 29 ga watan Rabi’ al-awwal 1442AH.

“Duk Musulmin da ya ga wata ya sanar da basaraken da ke kusa da shi domin sanar da Majalisar Sarkin Musulmi”, sanarwar.

Watan Rabi’us Sani shi ne wata na hudu a kalandar Musulunci wanda ke shekara ta 1442 Bayan Hijira.