✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Sarkin Musulmi ya bukaci Qausain TV ya kara himma

Sarkin Musulmi ya shawarci Kamfanin Talabijin na Qausain TV ya rubanya kokarinsa wajen wayar da al'umma

Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Muhmmad Sa’ad Abubakar ya shawarci Kamfanin Talabijin na Qausain TV da ya rubanya kokarinsa wajen isar da sako ga al’umma.

A yayin ziyarar da shugabannin Qausain TV suka kai masa, Sarkin Musulmin ya bukaci tashar da ta ci gaba da aiki tukuru bisa kwarewa kamar yadda aka san ta wajen wayar da kan al’umma da ilmantar da su ta hanyar shirye-shiryenta.

Sarkin Musulmi Sa’ad Abubakar ya kuma yaba bisa yadda tashar take yada shirye-shiryenta a harsuna guda uku da suka hada da Turanci da Hausa da kuma Larabci.

A cikin jawabinsa a yayin ziyarar, Shugaban Kamfanin Qausain TV, Alhaji Nasir Musa Albanin Agege, wanda ya jagoranci sauran shugabannin Kamfanin, ya gode wa Sarkin Musulmi bisa shawarwarin da ya ba su da kuma kyakkyawan tarbar da suka samu.

Ya kara da cewa, “za mu fara aiki da shawarwarin da suka fito daga uba kuma jagora a nan take wajen yada shirye-shiryenmu a kowane lokaci.”

Kazalika tawagar ta karrama Mai Alfarma Sarkin Musulmin da lambar yabo, sannan ta mika masa kyautar hoton girmamawa wanda ke dauke da hotonsa.

Daga karshen tawagar ta samu damar yin hoto na jam’i tare da Mai Alfarma Sarkin Musulmi da wasu daga cikin ’yan majalisarsa.