✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Sarkin Musulmi ya bukaci a inganta tsaro a hanyoyi

Mai alfarma Sarkin Musulmi Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar ya bukaci a karfafa harkokin tsaro a hanyoyin kasar nan, musamman ta hanyar tabbatar da ana bin…

Mai alfarma Sarkin Musulmi Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar ya bukaci a karfafa harkokin tsaro a hanyoyin kasar nan, musamman ta hanyar tabbatar da ana bin dokokin tuki domin kare rayuka da dukiyoyin al’umma.

Haka kuma ya bukaci manyan jami’an gwamnati da su rika fadakar da direbobin da ke cikin ayarinsu kan su rika bin dokokin hanya a yayin gudanar da ayyukansu na tuki a hanya.

Sarkin Musulmin ya bayyana haka ne a shekaranjiya, yayin da ya amshi bakuncin Kwamandan Shiyyar Sakkwato da Kebbi da Zamfara na Hukumar Kiyaye Hadurra ta kasa (FRSCN), Dokta Kayode Olagunju a fadarsa da ke Sakkwato.