Sarkin Musulmi Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar ya bayar da umarni a fara duban watan Rajab wanda ake kira watan Azumin Tsofaffi daga ranar Talata, 31 ga watan Disamba, 2024.
Kwanan watan ya zo daidai da 29 ga watan Jimada Assaniya, shekara 1446 bayan Hijira.
Shugaban kwamitin bayar da shawara kan harkokin addini a Fadar Sarkin musulmi, Wazirin Sakkwaato, Farfesa Sambo Wali Junaidu ne ya sanar da hakan a wata takarda da ya raba wa manema labarai.
Wazirin Sakkwato ya ce duk wanda ya samu ganin jinjinrin watan Rajab ya sanar da hakimi ko uban kasar da ke kusa da shi a nan ne za a kai maganar ga Sarkin Musulmi Muhammad Sa’ad Abubakar.
Ya roki Allah y a taimake su a cikin wannan aikin da suke yi na addini.