Mai Martaba Sarkin Kano, Alhaji Aminu Ado Bayero CFR na halartar wani bikin gargajiya da hawan dawakai a kasar Morocco.
Wakilinmu ya ruwaito cewa, Sarki Aminu na halatar bikin ne a birnin Marrakesh a bisa gayyata ta musamman a matsayin babban bako.
- HOTUNA: Ziyarar Sarkin Kano Da Na Bichi Ga Sarkin Musulmi
- Masarautar kasar Maroko ta gayyaci Sarkin kano ziyarar kwana 7
Sarkin ya isa birnin Marrakesh a ranar Lahadi a inda ya samu gagarumar tarba da abubuwan nishantarwa na gargajiyar kasar.
A rana Asabar ne Babban Jami’in Hulda da Al’umma na masarautar, Balarabe Kofar Na’isa ya fitar da sanarwar gayyatar Sarkin zuwa kasar a matsayin babban bako na bukukuwan gargajiyar.
Bikin gargajiyan na hawan dawakai yana da amfani da fa’idodi masu yawa wadanda suka hadar da bunkasar harkar noma, riko da dabbaka al’adun gargajiya da muhalli, da kuma wasanni a matsayin tushen nishadi.
Sannan kuma a cewar sanarwar, bikin na wannan shekara zai kunshi sabbin abubuwa da dama yayin da baki daga kasashen Afirka da dama za su halarta.
Tawagar sarkin ta hada da Alhaji Ahmad Ado Bayero, Sarkin Dawakin Tsakar Gida da Ambasada Ahmed Umar OON, Dan Malikin Kano, da Malam Isa Bayero, da kuma sauran wasu ma’aikatan fadar ta Kano.
Ana sa ran dai Sarkin zai dawo gida ranar Lahadi 23 ga Oktoba, 2022.