✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Sarkin Kano ya yi tsokaci kan darajar Naira

Mai Martaba Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi na biyu , ya bayyana gamsuwarsa da kamun ludayin gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari.A wata hira ta musamman da BBC…

Mai Martaba Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi na biyu , ya bayyana gamsuwarsa da kamun ludayin gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari.
A wata hira ta musamman da BBC a wata ziyara da ya kai Africa ta Kudu, Sarkin ya ce, gwamnatin Shugaba Buhari ta yi kokari wajen yaki da cin hanci da rashawa da kuma yaki da kungiyar Boko Haram, kuma dukkanin wadanann abubuwa ne da za su taimakawa tattalin arzikin kasa.
Sarkin Kano Muhammadu Sanusi na biyu, ya ce a matsayinsa na mai goyan bayan gwamnatin Muhammadu Buhari ya zama wajibi ya ba ta shawara ta sake duba manufarta a kan darajar Naira.
‘’A ra’ayi na ya kamata shugaban kasa ya sake duba shawarar da ya dauka kan batun darajar Naira, kuma matakin da babban bankin Najeriya ya dauka, na hana mutane su shigo da dalolinsu, abin da zai taimakawa tattalin arzikin kasar,” inji sarkin.
A karshe sarkin ya kuma jinjinawa shugaban kasar a matakan da ya dauka wajen yaki da rashawa da kuma gyara da ake yi a bangaren man fetur.