✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Sarkin Kano ya koka kan dabi’ar rashin karantun littafai a tsakanin matasa

Ya koka da yadda matasan yanzu suke bata lokaci a hira ta wayar salula da kuma intanet.

Mai Martaba Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero, ya koka kan dabi’ar rashin karatun littafai a wannan zamani.

Sarkin ya yi wannan koken ne a jawabinsa yayin bikin kaddamar da wani littafi na turanci mai suna ‘The Audacity of Hope’ a Abuja a ranar Asabar.

Sarkin na Kano wanda shi ne babban bako kuma uban taro, ya koka da yadda matasan yanzu ke karatun littafi kawai don ci jarrabawa.

Ya kuma koka da yadda matasan yanzu suke bata lokaci a hira ta wayar salula da kuma intanet.

“Hakika wannan ba zai haifar da da mai ido ba, a yanzu da kuma nan gaba, saboda hakan ba zai kawo wani ci gaba ta hanyar ilimi da kwazon su [matasan] ba,” in ji sarkin.

Mai martaba sarkin ya kuma yi kira ga masu ruwa da tsaki da su tashi tsaye, su kuma yi duk yadda za su yi wajen dakile wannan ci gaban mai hakar rijiya a tarbiyar matasan kasar nan.

Dangane da littafin da aka kaddamar, sarkin ya ce daga sunan littafin, hakan ya nuna cewa ya sha bamban da sauran littafan da suke nuna matan Afirka, musamman na Arewacin Najeriya a mummunan yanayi.

Sarkin ya kuma bayyana cewa, babu mamaki littafin zai zama abin nazari kan adabin Afirka, musamman a tsakanin malaman jami’o’i da kuma dalibai, bayan gushewar mata masu rubutu da harshen turanci, irinsu Zainab Alkali.