Mai martaba Sarkin Kano, Alhaji Aminu Ado Bayero CFR a wannan Lahadin ya ziyarci Jihar Kogi, inda ya mika ta’aziyyarsa ga iyalan marigayi mai martaba Ohinoyi na Kasar Ibira, Abdulkareem Ado Ibrahim.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun babban sakataren yada labaran gwamnan jihar, Mohammed Onogwu da aka rabawa manema labarai a Lokoja, babban birnin jihar.
- Isra’ila ta dakatar da Ministan da ya bukaci a ragargaza Gaza da nukiliya
- An yi garkuwa da matan shugaban karamar hukuma a Jigawa
Sanarwar ta ce Sarki Bayero ya jajanta wa gwamnan jihar, Alhaji Yahaya Bello da al’ummar Jihar Kogi bisa rasuwar Ohinoyi na kasar Ibira wanda ya riga mu gidan gaskiya a ranar 29 ga Oktoba, 2023.
Haka kuma, Aminiu Ado ya mika sakon ta’aziyyar masarautar Kano ga gwamna, gwamnati, da al’ummar jihar bisa rasuwar basaraken.
Hakazalika, Sarkin ya yaba wa Gwamna Bello bisa yadda yake inganta alaka mai karfi a tsakanin masarautu da sarakunan jihar.
A nasa jawabin, Gwamna Bello ya bayyana godiyarsa ga Sarkin da Masarautin Kano baki daya bisa jajen da suka yi da kuma kokarin bayar da goyon bayansu ga iyalan marigayi Ohinoyi na kasar Ibira.
Aminiya ta ruwaito cewa, Ohinoyi na Kasar Ibira ya koma ga Mahaliccinsa ne yana da shekaru 94 a duniya, kuma bayan shekaru 25 a karagar mulkin Masarautar Kasar Ibira da ke Jihar Kogi.
Ya hau mulki ne a shekarar 1997 bayan rasuwar Ohinoyi Sanni Omolori.