✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Sarkin Hausawan Agege ya rasa mahaifiya

Allah Ya yi wa Hajiya Adama Muhammad Dogonkaɗai rasuwa a ranar Alhamis (03-08-2017. Ita ce mahaifiyar Sarkin Hausawan Agege, Alhaji Musa Muhammad Dongokaɗai. Marigayiyar ta…

Allah Ya yi wa Hajiya Adama Muhammad Dogonkaɗai rasuwa a ranar Alhamis (03-08-2017. Ita ce mahaifiyar Sarkin Hausawan Agege, Alhaji Musa Muhammad Dongokaɗai.

Marigayiyar ta rasu ne tana da shekara 117, bayan ta yi fama da jinyar tsawan shekara tara. Ta rasu ta bar ’ya’ya biyu waɗanda suka haɗa da Sarkin Hausawan Agege, Alhaji Musa Muhammad Dogonkadai da ƙaninsa, Alhaji Abdullahi Muhammad Dogonkadai da jikoki tara da tattaba-kunne 20.

Tuni aka yi mata janaza kamar yadda Musulunci ya tanada. Allah Ya jikanta da rahama, amin.