✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Sarkin Hausawa ya shawarci ’yan Arewa a Kudu

Sarkin Hausawan Ibadan, Alhaji Ahmad dahiru Zungeru ya nemi dukan ’yan Arewa da ke zaune a Kudu maso Yammacin kasar nan su yi rajistar sunayensu…

Sarkin Hausawan Ibadan, Alhaji Ahmad dahiru Zungeru ya nemi dukan ’yan Arewa da ke zaune a Kudu maso Yammacin kasar nan su yi rajistar sunayensu da hadaddiyar kungiyar Ci Gaban Hausawa, (SAHC) wacce take fafutukar ci gabansu a wannan sashe.

Sarkin ya yi wannan kira ne a ranar Lahadin da ta gabata, jim kadan bayan mika takardun shaidar zaben sababbin shugabannin kungiyar reshen Jihar Oyo da aka gudanar a babban ofishin kungiyar da ke Kasuwar Bodija a Ibadan. Ya ce, “Gwagwarmaya da fafutikar kwato ’yanci da kungiyar take yi ga ’yan Arewa a wannan sashe ba za ta yi nasara ba muddin muka juya mata baya. Kamata ya yi dukanmu mu fito kwai da kwarkwata, mu shiga cikin wannan kungiya domin ci gaban al’ummarmu.”

Cikin jawaban manyan baki da suka hada da Sarkin Hausawan Akinyele, Alhaji Ado Sulaiman da Sarkin Fulanin Jihar Oyo Alhaji Muhammadu dan’ali da Shugaban Karar Shanu ta Akinyele Alhaji Audun Bukar da dan Malikin Jihar Oyo Alhaji Uba Bala, sun tabbatar da bayar da hadin kai da goyon baya ga kungiyar. Sun yi kira ga sababbin shugabannin kungiyar su ji tsoron Allah da kwatanta gaskiya da adalci wajen gudanar da jagorancin jama’a.

Sabon Shugaban kungiyar, Alhaji Ali danmeri, ya ce, “Dukan mambobin kungiyar sun ji dadin irin ayyukan da muka gudanar a cikin shekara 4 da suka wuce, shi ne dalilin da ya sa suka amince da sake zaben wadansu daga cikinmu domin ci gaba da yin irin wannan aiki a nan gaba.”

Ya ce “Babbar matsalar da muka fuskanta a baya ita ce, irin yadda gwamnatocin jihohi 6 na Kudu maso Yamma suka yi amfani da kungiyarmu wajen kyautata zamantakewa da samar da zama lafiya da kwanciyar hankali a tsakanin ’yan Arewa da kabilun Yarabawa amma daga baya suka yi watsi da mu. Ba mu samun tallafin komai daga gwamnatocin kamar yadda suke tallafa wa sauran kungiyoyi ba. Wannan ita ce babbar matsalarmu a yanzu da muke fata sarakunanmu za su yi mana jagorancin yin maganinta.” 

Sauran shugabannin kungiyar da aka zaba sun hada da Mataimakin Shugaba Alhaji Tukur Ahmed da Sakatare, Malam Idris Abdulra’uf da Ma’aji, Alhaji Mukhtari Garba da Sakataren Kudi, Abubakar Ibrahim da Mataimakin Sakatare, Ibrahim Garba da Sarkin Samarin Bodija, Alhaji Muhammed Sani Idris da aka zaba a matsayin Kakakin kungiyar.