Sarkin Fulanin Ilori, Usman Adamu Hardo, ya kubuta bayan kwana uku a hannun ’yan bindidar da suka yi garkuwa da shi a ranar.
Masu garkuwan sun lakada wa Ardo Usman duka tare da barazana ga rayuwarsa kafin su sako shi, lamarin da ya sa aka kai shi asibiti domin duba lafiyarsa.
Da yake tabbar da sako basaraken, Sarkin Fulanin Abeokuta, Alhaji Kabir Labar, wanda dan uwan Sarkin Fulanin na Ilori ne, ya ce, “Ya saba taimakon jami’an tsaro a Jihar Kwara wajen yakar garkuwa da mutane da sauran matsalolin tsaro.
“Shi ne ya taimaka aka kama wadanda suka yi garkuwa da wasu ’yan kasar waje da ke aikin gyaran titi a Jihar Kwara a kwanankin baya.
“’Yan bindigar sun dade suna bibiyar shi kuma sun so su kashe shi ne, amma Allah Ya tsare shi saboda yawan addu’ar neman tsari daga gare su.
“Ya shaida mana cewa sun dauke shi ne a motarsu a Ilori, bayan sun yi tafiya na kilomitoci, sai da suka kai wani daji sai wasu babura hudu suka zo suka dauke su suka shige da su cikin jeji.
“Sun rufe masa ido ba su bude masa idanu ba sai da suka kai maboyarsu da almurun ranar da suka sace shi [Alhamis].
“Sun yi ta razana shi da harbe-harbe kuma ba su ba su wani abinci ba sai garin rogo”, inji shi.
Ya kara da cewa sai da masu garkuwar suka yi mahawar ka ko su kashe ardon, kafin daga bisani su sake shi.
“Suka kai shi gefen titin a hanyar Madatsar Ruwa ta Kainji, inda a nan wasu mutane suka tsince shi suka kai shi wani ofishin ’yan sanda a garin Mokwa na Jihar Neja.
“Daga nan nan aka garzaya da shi zuwa asibiti kafin a koma da shi zuwa Ilori a ranar Litinin”, kamar yadda ya yi bayani.
Dan uwan ardon ya ce basaraken ya yi wa ’yan sanda a Ilori bayanin abun da ya faru har ya ziyarci Sarkin Ilori kafin ya karasa gida.
Ya ce duk da cewa ’yan bindigar ba su nemi kudin fansa daga iyalan ardon ba, amma sun yi tafi da tsabar kudin da ke tare da shi a lokacin da suka sace shi kusan Naira miliyan 11.