Mai martaba Sarkin Dutse Alhaji Nuhu Muhammed Sunusi ya nuna takaicinsa kan yadda karatu yake wahala a halin yanzu, sabanin yadda abin yake a baya da gwamnati ke wa dalibai komai.
Mai Martaba sarkin ya fadi haka ne a lokacin da makaranatar Kwalejin Gwamnati ta Birnin Kudu ta gudanar da taron tsofaffin dalibanta na shekara- shekara a harabar makarantar da ke garin Birnin Kudu.
Sarkin ya ce a wancan lokacin dalibai suna kiyaye dokokin makaranata, ba sa wasa da kayan karatu ko lalatasu, amma yanzu babu gata a harkar karatun kuma daliban suna yawan karya kujerun da gadajan kwanan dalibai.
Saboda haka ne sarkin ya hori daliban da su kiyaye wajen barnata kujerun karatu da sauran kayan makaranta domin ita hukuma da kuma kungiyar tsofaffin dalibai duk fafutikar da suke yi kullum shi ne su gyara makarantar. Sannan kuma suna yi ne dominsu.
A yayin taron, an bayyana cewa tsohon Gwamna Sule Lamido ya ba hukumar gudanarwar taron kungiyar BIKOBA gudunmawar Naira miliyan daya wanda a ka yi amfani da shi wajen ciyarwa da walwalar mutanen da suka halarci taron. Sannan an sami kudin gudunmawa daga manyan mutane na sama da naira 200,000, kuma an sayar da riguna da sauran abubuwa masu dauke da tambarin kunigiyar wanda hukumar makarantar da kungiyar ta BIKOBA ta sami kudin shiga mai yawa ta dalilin hakan.
Da yake nasa jawabin, shugaban makarantar na yanzu malam Haruna Muhammad Bashir ya ce an bude makarantar da dalibai 30 a matsayin Firamare ta kwana a shekarar 1951, sannan daga aka daga darajarta a shekarar 1960.
Makarantar ta yaye dalibai da yawa ciki har da gwamnoni shida da suka hada da Alhaji abubakar Rimi da Janar Lawal Jafaru Isah, da Barista Ali Sa’adu da Sule Lamido, da Alhaji Abdullahi Umar Ganduje da Alhaji Badaru Abubakar. Da manyan sarakuna kamar su Sarkin Dutse Alhaji Nuhu Muhammed Sunusi, da manyan ‘yan kasuwa kamar Alhaji Aliko dangote da dai sauransu.
Shugaban makarantar ya ce kungiyar ta BIKOBA da gwamnatin Jihar Jigawa sun taimakawa makarantar da teburan karatu masu daukar dalibai uku guda 405 da gadajan kwanan dalibai guda 250 da teburan malamai 18 tare da gidajan sauro masu magani guda 2,500, sannan sun gina bandaki guda 10 da fanfom tuka-tuka guda 3 domin anfanin daliban makarantar.
Da yake nasa bayanin, shugaban kungiyar BIKOBA Malam Nuhu Isah Abdullahi ya ce kungiyar ta ware sama da Naira miliyan N38,180,500.00 domin aiwatar da muhimman ayyuka a cikin makarantar, sannan ya yaba wa Gwamnan Jihar Kano Alhaji Abdullahi Umar Ganduje bisa kokarin da yake na taimakon kungiyar