✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Sarkin Dutse na da hujjar yin sujuda

Mai yiwuwa zuwa yanzu mai karatu ka ga hoton mai MartabaSarkin Dutse Alhaji Muhammadu Nuhu Sanusi,a shfi na 19, awannan jarida ta makon jiya ya…

Mai yiwuwa zuwa yanzu mai karatu ka ga hoton mai MartabaSarkin Dutse Alhaji Muhammadu Nuhu Sanusi,a shfi na 19, awannan jarida ta makon jiya ya fadi yana sujada a cikin kasa a sabon filin jirgin saman kasa da kasa na Dutse babban birnin Jihar ta Jigawa, a gaban Gwamnan jihar Alhaji Sule Lamido dawasu jami`an gwamnatin jihar da na Kamfanin wani jirgin sama.Abin da ya kawo wannan sujada shi ne, saukar gwaji da babban jirgin saman nan kirar 747, ya yi a filin jirgin saman a ranar Asabat 30-08-14. Filin jirgin saman da a bana ba wai Maniyatan jihar ta Jigawa daga nan suke tashi zuwa aikin Hajjin bana ba, a`a, a nan aka yi bikin tashin ayarin farko na Maniyatan kasar nan na bana.
Ita irin waccan sujada Malamai sun ruwaito cewa akan yi tabakatatan a duk lokacin da wani abun farin ciki ya samu mutum, muddin yana da alwala, to, zai iya faduwa kasa warwas ya yi sujada koda kuwa cikin laka da tabo yake, a zaman ya gode wa Allah bisa ga ni`imar da Allah Ya yi masa. Bugu da kari Malaman suka cewa nuna irin wannan godiya ta hanyar sujada, Allah kan yi murna da bawanSa, sannan kuma zai iya kara nunnunka masa wasu ni`imomin, don Allah Yana son masu godemaSa.
  Gwamnatin mulkin soja ta tsohon shugaban kasa Janar Ibrahim Babangida ita ta kirkiro jihar Jigawa a ranar 27 ga Agustan1991, daga cikin tsohuwar jihar Kano, yau shekaru 23 da kwanaki 12, daidai. Tun kirkirota, jihar take cikin mawuyacin hali irin na adawar yadda garin Dutse  Gadawur zai kasancebabban birnin jihar? Alhali ga manyan garuruwan Sarakunan yanka masu daraja ta daya irinsu Hadeja da Kazaure da Gumel, alhali a lokacin Dutsen tana masarautar Hakimi a karkashin masarautar Kano (bayan kirkiro jihar ne aka kirkiro masarautun Dutse da Ringim).
Koda a wancan lokacin gudumar Dutsen, tana daga cikin gundumomin hakiman masarautar Kano da suke kusan koma baya akan kowane irin ayyukan ci gaba, kai hatta Sakatariyar karamar Hukumar  ta Dutse a mazauninta zaizayar kasa ke magine-ginenta barazana, kar ka yi batun ka ce abubuwan more jindadin rayuwa irin su wutar lantarki ko wani babban assibiti kowata babbar makarantar gaba da Sakandare, ko wasu manyan gine-gine, walau na jama`a ko na hukuma kamar yadda ake da su a garin Birnin Kudu da yake garin Hakimi, ko wadancan, amma sai ga matsayin da Allah Ya ba Dutse na zama babban birnin sabuwar jihar Jigawa. Wancan zalunci da wasu `yan asalin jihar suke ganin an yi masu, ya sanya har zanga-zangar nuna fushi wasu mutanen masarautar Hadeja suka gudanar da fatan gwamnatin mulkin sojan za ta gyara, amma ina bakin alkami ya riga ya bushe.
Wannan arziki da Allah Ya yi wa Dutse ya sanya a wancan lokacin mutane a cikin zance kan ce “Allah Kai mana arziki irin na Dutse.” Ko kusa mai karatu kar ka dauka cewa mutanen Hadeja kadai suka nuna adawarsu akan ajiye babban birnin jiharsu a Dutse, a`a su ma mutanen sauran masarautun ma sun nuna, kai hatta wasu talakawa na Garu, wato tsohon garin Dutse sun nuna adawarsu akan suna ganin hakan zai sa a kwace masu gonakin noma da suka gada iyaye da kakanni.
A irin wannan hali ne Kantoman mulkin soja na farko na jiharKanar Olayinka Sule, wanda a lokacin yake Kwamandar Birgedta uku a Kano ya fara kafa harsashin zaman Dutse babban birninjihar Jigawa, wanda ka iya cewa a zamansa na watanni uku koma`aikata bai gama ganin zamansu ba aka yi zaben gwamnanfarar hula na farko da `yan Majalisun Dokoki na shekarar 1991,wanda Barista Ali Sa`ad Birnin Kudu ya samu nasarar zama gwamnan farar hula na farko a  Jigawa a farkon watanJanairun 1992. Shi ma Barista Ali Sa`ad ko shekara biyu bai cika ba Janar Abacha ya hambarar da gwamnati rikon kwarya ta kusan watanni hudu ta Cif Enest Shonekan a cikin watan Nuwamban 1993, soja ya dawo mulki a watan Nuwambar 1993,wanda ya rusa mulkin angulu da kan zabon da Janar Babangidaya nemi jarrabawa.
  Tabbatas gwamnonin mulkin soja da suka samu kansu cikinmulkin jihar Jigawa irin su Kanar Ibrahim Aliyu da Kanar Rashid Shokoni da Kanar Zakariya Maimalari, duk sun taka rawarsu gwargwadon zarafi wajen ganin an samu kafa kyakykyawan harsashin gina jihar, amma ka iya cewa siyasar rmasarauta da irin ganin rashin cancantar Dutse babban birnin jiha, da suka dauko asali tun farkon kafa jihar ta sanya abubuwa suka dabaibaye jihar  ta yadda ci gaban da ake tsammani ya faskara, ma`aikatan gwamnati suka rinka zama kafar ungulu, don haka aka zauna tsawon shekaru ba inda aka raya, wasu ma na ganin gobe-gobe za a canja babban birnin jihar daga Dutse zuwa wani garin.
Shigowar jamhuriya ta hudun nan a shekarar 1999, aka yi ta fatan   ganin abubuwa za su inganta a karkashin gwamnatin Alhaji Ibrahim Saminu Turaki da ake ganin matashi ne da ya san siyasar kasashen duniya ta ci gaba, amma ina! Shi ma sai yabullo da nasa tsarin da ya kara tarwatsa jihar, ta hanyar rarraba Ma`aikatu da Hukumomi da Kamfanoni gwamnatin jihar zuwa garuruwan jihar daban-daban. Allah jikan mataimakinsa na wancan lokacin Alhaji Ibrahim Shehu Kwatalo, wanda a wata hira da muka yi da shi akan waccan tsari, yake kare shi da cewa“Muna kokarin mu kauce wa tsarin tsohuwar jihar Kano da aka yi ta ajiye duk wasu abubuwan ci gaban jihar a Kanon, aka yi watsi da sauran garuruwa, so muke garuruwanmu su tashi kafada-da-kafada da babban birnin jiharmu”. In ji tsohon mataimakin gwamna Kwatalo. Ko kadan ba cewa nike yi ba tsohon gwamna Saminu Turaki bai yi kome ba a Jigawa, a`a, kamar yadda `yan Jigawar suka sha fada damar da ya samu bai yi amfani da ita ba kamar yadda ya kamata.
Amma zuwan Alhaji Sule Lamido cikin wadannan shekaru bakwai da watanni kusan hudu, kowa ya je Dutse, ya san ta canja, ta kuma fara amsa sunan babban birnin jiha. Ba wai so nike in ce ya yi kaza, ya yi kaza ba, a`a, yadda ban ambaci ayyukan gwamnonin da suka rigaye shi ba, shi ma   ba zan kawo nasa ba. Amma dai daga irin yadda Dutsen ta fara bunkasa, har a yau ga filin jirgin saman kasa da kasa a cikinta, kasan cewa addu`o`i da begen da wasu suka dade suna yi na ganin komen daren dadewa za a canja babban birnin jihar daga garin Dutse zuwa wani garin ya zama mafarki. Don haka mai martaba Sarkinna Dutse yana da hujjar yin sujjada a bainar jama`a cikin birji don gode wa Allah akan wannan baiwa da  Ya yi wa kasarsa, kuma zamanin mulkinsa .