Sarkin Kano Muhammadu Sunusi II ya isa gidan Gwamnatin jihar da safiyar Juma’a gabanin mika masa takardar fara aiki bayan dawo da shi kan kujerarsa.
Su ma hakiman Masarautar Kano sun riga sun hallara a fadar gwamnatin domin mika mubaya’arsu ga Sarki Sanusi II.
Aminiya ta gano ranar Alhamis da dare Sanusi II ya dawo Kano a sirranci cikin tsauraran matakan tsaro, inda ya kwana a gidan gwamnati.
A halin yanzu an kammala shirye-shirye fara bikin mika masa takardar aiki, inda a karon farko za gan shi a bainar jama’a tun bayan sanar da nadin nasa.
- Yaudara da radadin tsadar rayuwa a Mulkin Tinubu
- Kotu ta dakatar da rushe masarautun Kano
- NAJERIYA A YAU: Abu Na Gaba Da Zai Faru Da Sarakunan Kano Da Aka Tuɓe
Za a gudanar masa da hawa daba sanan ya wuce zuwa fadar sarki da ke Nassarawa kafin daga bisani ya jagoranci Sallar Juma’a a Masallacin Fadar Sarkin Kano da ke Kofar Kudu.
Dawarsan ta kasance ne bayan Gwamna Abba Kabir ya sanar da dawo da shi kan kujerar Sarkin Kano a matsayin sarki daya tilo a jihar.
Gwamna Abba ya sanar da haka ne bayan sanya hannu a bisa sabuwar dokar masarautin jihar, wadda ta rushe sabbin masarautu biyar da tsohuwar Gwamnatin Ganduje ta kirkiro shekaru hudu da suka gabata.