✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Meshaal ya zama Sarkin Kuwait bayan rasuwar Sarki Nawaf

Allah Ya yi wa Sarkin Kuwait Sheikh Nawaf al-Ahmad al-Jaber al-Sabah rayuwa bayan shekaru uku da hawa mulki

Sarkin Kuwait, Sheikh Nawaf al-Ahmad al-Jaber al-Sabah ya rasu yana da shekaru 86 a duniya.

Mataimakin Firaministan kasar, Issa Al-Kandari, ya tabbatar da rasuwar, da kuma ɗan uwansa Sheikh Meshaal al-Ahmad al-Jaber al-Sabah, mai shekaru 83 a matsayin sabon sarkin kasar.

Sabon sarkin, Sheikh Meshaal al-Ahmad al-Jaber al-Sabah ya kasance na hannun damansa, kuma ya sha kasancewa mukaddashinsa a lokutan da Sarki Nawaf ke duba lafiyarsa.

Gwamnatin Kuwait ba ta bayyana dalilin rasuwar Sarki Nawaf ba, amma ta sanar da hutun aiki na kwana uku da kuma juyayin rasuwarsa na tsawo kwana 40.

Allah Ya yi wa Sheikh Nawaf rasuwa ne bayan shekaru uku da hawansu kan karagar mulki.

A shekarar 2020 aka rantsar da shi bayan rasuwar dan uwansa, Sheikh Sabah al-Ahmad al-Jaber al-Sabah, wanda ya rasu a kasar Amurka yana da shekaru 91 a duniya.

A watan Nuwamba ne dai aka kwantar da Sheikh Nawaf a asibiti sakamakon fama da matsanancin rashin lafiya.

Sheikh Meshaal al-Ahmad al-Jaber al-Sabah ya zama Sarkin Kuwait yana da shekaru 83
Sheikh Meshaal al-Ahmad al-Jaber al-Sabah, ya zama Sarkin Kuwait yana da shekaru 83. (Hoto: Reuters)

Sabon sarkin ya kasance Yarima Mai Jiran Gado ga Sarki Nawaf.

Marigayi Sarki Nawaf ya kasance tsohon Ministan tsaro da kuma ministan harkokin cikin gida sannan a shekarar 2006 ya zama yarima mai jiran gado.

Ya jagoranci ƙasar a lokacinvda ta ta ya fama da matsalar tattalin arziki sakamakon faduwar farashin danyen mai a kasuwar duniya da annobar COVID-19 da sauransu.

Sauye-sauyen da ya kawo sun hada da afuwa ga masu laifi, sakin  fursunonin siyasa, ba da shaidar zaman kasar da kuma zaben ’yan majalisa