✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An kama dalibi da bindiga a Jami’ar ATBU

Jami'an tsaro sun damke wani dalibi a Jami'ar Abubakar Tafawa Balewa (ATBU) da ke Jihar Bauchi dauke da bindiga da harsashi.

Jami’an tsaro sun damke wani dalibi a Jami’ar Abubakar Tafawa Balewa (ATBU) da ke Jihar Bauchi dauke da bindiga da harsashi.

Dalibin dan aji 3 uku ne, kuma ’yan sanda sun cafke shi ne da bindigar  hannu ce bayan ya fito daga harabar jami’ar da ita,

Kakakin ’yan sandan jihar, Mohammed Wakil ya ce ana kama dalibin ne a lokacin da yake kokarin hada wasu gungun dalibai.

Wakil ya ce dalibin ya gaya musu cewa hayar bindigar ya karbo na shekarar karatu guda daga wurin wani.

Dalibin ya shaida musu cewa ya karbo bindigar ce domin kare kansa daga masu aikata muggan laifuka.

Jami’in ya ce Kwamishinan ’yan sandan jihar, Auwal Mohammed Musa, ya ba da umarnin gudanar da bincike domin gano ainihin dalilin dalibin na mallakar bindigar da kuma ko ya taba amfani da ita sannan a gurfanar da shi a gaban kotu.