✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Sarki Charles ya karɓi baƙuncin Tinubu a Fadar Buckingham

Tinubu ya ƙara nanata ƙudurin Nijeriya na yaƙi da matsalolin sauyin yanayi.

Sarkin Ingila, Charles III ya karɓi baƙuncin Shugaba Bola Tinubu a Fadar Buckingham da ke birnin Landan.

Mai magana da yawun shugaban ƙasa, Bayo Onanuga, shi ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Alhamis.

Sanarwar ta bayyana ganawar da aka yi ranar Laraba a matsayin ta sirri, wadda ta ƙara nuna alaƙar da ke tsakanin Nijeriya da Birtaniya.

“Shugabannin sun tattauna batutuwan da suka shafi ƙasashensu, musamman matsalar sauyin yanayi,” kamar yadda sanarwar ta bayyana.

Ya ƙara da cewa Shugaba Tinubu da Sarki Charles sun tattauna hanyoyin da za su iya haɗa gwiwa musamman a daidai lokacin da ake shirin taron saunyin yanayi na COP 29 da ke tafe a ƙasar Azerbaijan da kuma taron ƙasashe rainon Ingila wato CHOGM da za a yi a Samoa.

Ya ce: “Tinubu ya ƙara nanata ƙudurin Nijeriya na yaƙi da matsalolin sauyin yanayi a irin yanayin da zai yi daidai da tsare-tsaren makamashin ƙasar.”

Wannan ne karo na biyu da shugabannin suka gana bayan ganawarsu ta farko a Dubai a taron COP 28 na bara.

Richard Montgomery, Jakadan Birtaniya a Nijeriya wanda ya tarbi Shugaba Tinubu yayin isowarsa Fadar Buckingham