Hukumar Hisbah a Jihar Kano ta gayyaci Sarauniyar Kyau ta Najeriya ta 2021, Shatu Garko, ofishinta don amsa tambayoyi game da shigar ta gasar.
Shugaban hukumar, Sheikh Haroun Ibn Sina ne ya sanar da da manema labarai hakan a Kano, a ranar Laraba.
- An damke masu yi wa ’yan bindiga safarar karuwai
- An cafke ’yar aikin da ta kashe mahaifiyar tsohon Gwamnan Edo
Shatu mai shekara 18 a duniya ta doke ’yan mata 17 da suka yi takara tare wajen zama gwarzuwar gasar sarauniyar kyau, kuma mace ta farko wadda ci gasar sanye da hijabi tun bayan fara gasar shekara 44 da suka gabata.
“Mun tabbatar da cewa Shatu Garko Musulma ce ita da iyayenta daga Karamar Hukumar Garko a Jihar Kano, kuma Kano gari ne na Musulunci don haka ba za mu bari lamarin ya tafi haka nan ba.
“Za mu gayyaci iyayenta da kuma ita don jin dalilin da ya sa suka bari ’yarsu ta shiga abin da ya saba wa addinin Musulunci,” cewar Ibn Sina.
Ya ce Hisbah ta gayyaci iyayen Shatu ne domin sanar da su matsayar addinin Musulunci game da gasar da ’yarsu ta shiga ta sarauniyar kyau.
Ibn Sina ya yi karin haske kan lamarin, inda ya jawo wasu ayoyi daga Alkur’ani mai girma.
“Ubangiji ya sanar a cikin Alkur’ani mai girma cewa, Manzon Allah Ya sanar da matansa, ’yavyansa mata da su kame tare da rufe jikinsu yadda ya kamata.
“Sannan wasu ayoyi a Alkur’ani sun bayyana cewa, Ubangiji Ya umarci mutane da su guji aikata laifuka da idanunsu ta hanyar kallon jikin mutane, sannan mata su killace jikinsu, fuskokinsu — kafafu da hannaye kadai aka yarda su bayyana.”