Rahotanni daga Fadar Buckingham da ke Birtaniya, sun tabbatar da cewa Sarauniyar Ingila, Elizabeth II ta kamu da cutar Coronavirus.
A yanzu Sarauniyar Ingila ita ce mutum ta baya bayan nan daga cikin mashahuran shugabannin duniya da cutar ta harba.
- BIDIYO: Mun ga mutanen da ba su taba ganin N5,000 ba – Minista Sadiya
- Harin Sojin Najeriya kan ’yan bindiga ya yi kuskuren kashe yara 7 a Nijar
Wannan dai na zuwa ne yayin da Sarauniya Elizabeth mai shekara 95 ta hadu da babban danta kuma magajinta, Yarima Charles wanda ya sake kamuwa da cutar karo na biyu a makon jiya.
Fadar Buckingham ta bayyana cewa sarauniya na tattare da alamun sanyi amma ana sa ran za ta ci gaba da gudanar da ayyukanta sama-sama a Windsor a mako mai zuwa.
“Za a ci gaba da duba lafiyarta kuma za a bi duka hanyoyin da suka dace,” kamar yadda fadar ta bayyana a wata sanarwa da ta fitar.
Sanarwar na zuwa ne mako guda bayan da sarauniyar ta kafa tarihi ta zama wadda ta fi dadewa kan karagar mulki a tarihin Masarautar Ingila bayan ta cika shekara 70 a kan mulki a ranar 6 ga watan Fabrairu.
BBC ya ruwaito cewa babu shakka sarauniya an yi mata riga-kafin coronavirus zagaye na farko da na biyu.
Bayanai sun ce Sarauniyar tana bin rayuwa a hankali a ’yan kwanakin nan tun da ta kwana a asibiti a Oktobar bara yayin da ta je duba lafiyarta.