Sarkin Kano, Alhaji Aminu Ado Bayero, ya yi wata ganawar sirri da Sarkin Katsina, Alhaji Abdulmumini Kabir Usman, game da murabus din Wazirin Katsina, Farfesa Abubakar Sani Lugga.
Sarakunan biyu sun sa labule ne a Fadar Sarkin Katsina a ranar Lahadi, inda suka shafe awa biyu suna ganawa.
- ‘Rikicin Rasha da Ukraine zai kawo tsadar burodi a Najeriya’
- NAJERIYA A YAU: Yadda Sabuwar Dokar Zabe Za Ta Shafi Gudanar da Zaben Najeriya
Wata majiya ta ce Sarkin Kano ya ziyarci Sarkin na Katsina ne da yawun Majalisar Koli ta Harkokin Addinin Musulunci ta Najeriya (NSCIA).
Idan ba a manta ba, a ranar 14 ga watan Fabrairun 2022 ne Farfesa Sani Abubakar Lugga ya yi wani jawabi a wurin wani taro da ya halarta a Ilorin, babban birnin Jihar Kwara, inda ya koka a game da yadda matsalar tsaro ta addabi Najeriya, musamman Jihar ta Katsina.
Bayan taron ne Masarautar Kastina ta aike masa da takardar neman bahasi kan jawabin nasa, musamman a kan abubuwa uku da ya shaida wa taron, wadanda bisa alamu masarautar ba ta ji dadi ba.
Masarautar ta nemi ya bayyana hujjar jawabin da ya yi cewa makarantu da sauran cibiyoyin ilimi da ke wasu kananan hukumomi takwas na jihar suna fuskantar barazanar tsaro.
Sai kuma cewa da ya yi rashin tsaro ya tilasta wa wasu Hakimai daga kananan hukumomin takwas komawa Katsina, hedikwatar jihar da zama.
Sai kuma shaida wa taron da ya yi cewa a tsawon shekara daya da rabi da suka gabata, kusan kullum sai an kashe akalla mutum daya a Jihar Katsina.
Majiyoyi sun bayyana cewa wadannan abubuwa da Wazirin ya bayyana wa taron dai ba su yi wa masarautar dadi ba.
Amma a martaninsa ga takardar da masarautar ta aike masa, Farfesa Lugga ya bayyana wa mata cewa ya yi jawabin ne a matsayinsa na dan Najeriya, ba da yawunta ba.
Sannan ya hada takardar martanin nasa da takardar sauka daga matsayinsa na Wazirin Katsina.
Wata majiya ta shaida wa wakilinmu cewa a kan haka ne wasu manyan Sarakunan Arewa suka wakilta Sarkin Kano ya sa baki a batun na ajiye mukamin Wazirin Katsina da Farfesa Lugga ya yi.
Sai dai bayan tattaunawar ta awa biyu da ya yi da Sarkin Katsina, babu wani bayani game da ko an cim-ma wata matsaya a kan al’amarin.
Amma majiyarmu ta ce ziyarar ta Sarkin Kano babbar alama ce da ke nuna za a samu kyakkyawan sakamako.
Bayan ganawar sarakunan ne dai Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero ya kama hanyarsa ta komawa gida daga Katsina da misalin karfe uku na rana.