Sarakunan Arewacin Najeriya na gudanar taro kan rikice-rikce da suka kira “haukar mutane masu kashe juna” a yankin da ma fadin Najeriya.
Taron da ke gudana a Kaduna Karkashin jagorancin Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Muhammad Sa’ad Abubakar III, na kokari ne wajen lalubo mafita ga karuwar matsalar tsaro da ke addabar yankin da ma fadin Najeriya.
- Sojoji sun karkashe mayakan Boko Haram sun kubutar da kananan yara
- COVID-19 na neman yada cutar kyanda a Najeriya
Sarakunan za su kuma tattauna kan irin tasirin da illar da bullar cutar coronavirus ta yi wa rayuwar jama’a, da nufin bayar da shawarwari kan yadda za yi wa tufkar hanci.
Idan ba a manta ba, a makonnin bayan, Sarkin Musulmi ya ziyarci Gwamnan Jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai, inda muka kawo muku rahoton cewa sun tattauna ne a kan batun tsaro a jihar da sauran al’amura.
Bayan ganawarsu, El-Rufai ya shaida wa manema labarai cewa Sarkin Musulmi ya ba shi shawarwari kan hanyoyin shawo kan matsalar rashin tsaro a jihar, musamman ganin yadda rikicin kabilanci a Kudancin Kaduna ke damun mutane a fadin Najeriya.
Yankin Arewacin Najeriya na fama da matsalolin tsaro da suka hada da na kungiyar Boko Haram da ake faman yaki da ita tun a shekarar 2009.
A baya-bayan nan sojoji sun sanar da tarwatsa masana’ar makamai tare da kama daruruwan iyalan ‘yan kungiyar Darul Salam a Jihar Nasarawa, lamarin da masana ke cewa wata barazanar tsaro ce da ke bukatar a sa ido sosai a kai.
Ayyukan ‘yan bindiga da masu garkuwa da mutane musamman a Arewa masu Gabas da Arewa ta Tsakiya na cikin manyan matsalolin yankin, inda rikicin manoma da makiyaya ya zama tamkar ruwar dare.