✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Saraki da Tambuwal ba za su koma PDP- Badaru

Shugaban Kwamitin taron jam’iyyar APC na kasa, gwamnan Jihar Jigawa Abubakar Badaru ya ce Shugaban Majalisar Dattawa Bukola Saraki da Gwamnan Jihar Sakkwato Aminu Waziri…

Shugaban Kwamitin taron jam’iyyar APC na kasa, gwamnan Jihar Jigawa Abubakar Badaru ya ce Shugaban Majalisar Dattawa Bukola Saraki da Gwamnan Jihar Sakkwato Aminu Waziri Tambuwal ba za su koma PDP ba.

Badaru ya yi wannan jawabin ne a fadar Shugaban Kasa a ranar Litinin bayan ya gana da Shugaban Ma’aikatan Shugaban Kasa, Abba Kyari.

Badaru ya karyata rade-radin ne wanda ake yadawa, inda ya ce, “ba gaskiya bane wai Saraki da Tambuwal za su koma PDP. Kwanakin baya ma haka ake ta rade-radin cewa Gwamnan Jihar Binuwei zai bar APC, amma kuma daga bisani ya fito ya karyata maganar a taronmu na masu ruwa da tsaki.

“A dunkulw muke. Muna tare da Gwamna Tambuwal da Sanata Bukola Saraki kuma ba mu ko tunanin cewa suna tattaunawa da wata jam’iyya.”

Hakanan kuma gwamnan ya nuna cewa taron jam’iyyar APC na kasa da za a yi, za a yi shi ne cikin lumana, sannan kuma taron zai hada kansu waje guda.