Babbar Kotun Tarayya da ke zamanta a Kano ta ce Hukumar Sauraren Korafe-Korafe da Yaki da Cin Hanci da Rashawa ta Jihar na da damar binciken tsohon Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II.
Tun a watan Maris ne tsohon sarkin ya shigar da kara gaban kotun yana neman ta hana Hukumar binciken da ta fara kan zargin da ake masa na hannu a badakalar sayar da filin Gandun Sarki, mallakar Masarautar Kano.
Wadanda tsohon sarkin ke kara sun hada da Hukumar Karbar Korafe-Korafen da Shugabanta Barista Muhuyi Magaji Rimingado da Babban Mai Shari’a na Jihar Kano da Gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje.
A zamanta na ranar Talata, Kotun karkashin jagorancin Mai Shari’a Lewis Allagoa ta ce Hukumar ta Muhyi za ta iya fara gudanar da bincikenta a kan tsohon Sarkin.
Barista Muhyi ya bayyana cewa Hukumarsa na binciken tsohon Sarkin ne bisa zargin sa da hanmun cikin badakalar filayen Masarautar Kano da darajarsu ta kai Naira biliyan biyu da miliyan 200.