Santala kwaiduwa ta shiga cikin jerin manyan matan Haurobiya masu rike da mukaman hukuma, da suka shahara wajen kassara kasar nan. Wadannan mata dai idan har ba ku ari faden Malam Mantau ba, za ku iya fasko cewa sun hada da ’Yardidi da Araruma, wadanda suka yi rugu-rugu da kasuwar ririta jaririn jari. Ita kuwa Santala kwaiduwa, shugaba ce a harkar sufurin tsuntsayen sama, don haka ta sake su sakaka sai wuntsulowa suke ta yi, suna kassara rayuwa al’ummar Haurobiya.
Farfesun Borin Shorido shi ya fara kado tsuntsayen sama, bayan kafuwar mulkin dama-dama-da-kurda-kurda a kasar Haurobiya, inda a zamanin shangabansa, Balbelar Bi’u da shamuwar Somaliya mai shan sholisho da babban tsuntsun mai dauke da haruffa AaDaCa suka salwantar da rayuwar al’uma, cikin har da Babban mutum mai rawuna na birnin shehu, kuma shugaban Masu Fuskantar alkibla don kadaita Mahalcci da ibada a kasar Haurobiya. Da Farfesun Borin-shorido ya yi ta kado tsuntsaye babu kakkautawa, sai kawai Shugaban kasar Haurobiya na wancan zamanin, Baba-Ojo Mai Gonakin Ottawa ya sauke shi daga mukaminsa, inda ya nada Fufuken fankan-fayau, sai aka dan samu tsahirtawar wannan musifa.
Alkafura da wuntsula gudi-gudin tsuntsayen sama na daga cikin musifun da ke daga wa Haurobiyawa hankali, tun sa’adda Jam’iyya mai dan boto da sanda jirge ta kama ragamar mulkin kasar. Abin tambaya a nan, shim ne, tunda Baba-Ojo, ya taba ingiza keyar Farfesun Borin Shorido, me ya sa aka kasa yi wa Santala kwaiduwa komai kan yawan tsuntsayen da ta kado, tun kafin a sake kwata irin ta zamanin Farfesun Borin-Shorido?
A batu na waskiya, ni ma ban goyi bayan a wancakalar da Santalla ba, domin ita ‘Santaleliyar kwaiduwar kwan tsuntsaye ce,’ kun ga ke nan a fahimtar Shagaba Jatau- Mai-Sa-in-sa, wanda ya nadata a kan mukaminta, don ta ji dadin Gudun-loko da mahayan tsuntsayen sama, ya mika mata wuka da nama, ta yadda idan ta wancakalar da rayuka da dukiyoyi, ai a cikin kwaiduwa ake kyankeshe tsuntsu, sai kawai ta sake kyankyashe wa kasar Haurobiya wasu tsuntsayen. Ku dai sha kuruminku, kada ku ga Su Dauda-mai-maki da Tumbin-wulli sun gaza katabus a kan Santalla. Watakila ta yi musu alkawarin kanzon kurege, cewa daukacin tsuntsayen da Farfesun Borin-Shorido ya kakabo daga sama, za ta hada da nata, ta kyankyashe wasu masu ‘nagarta.’ To kun ji!
Saboda kwarewar aiki da kwazon kassara Arewa, Santala ta hana manyan tsuntsaye sufuri na kasahen Larabawa shawagi da sauka a birnin Dabo. Tana yawan aiwatar da ayyukan balbalta filayen saukar ungulaye da shaho da mujiya da shamuya da jemage da ke fadin Arewacin Haurobiya. Matar da ta kware a irin wadannan ayyuka, don me kuke bukatar ganin an ingiza keyarta ta yi gaba.
Ita Santalar nan da mujallu da mukallu da jaridun kasar Hauobiya ke dibge da labaranta ta kware a fannoni da dama, inda samu lambar yabo ta duniya a kwashi-kwaraf da dukiyar Haurobiya. Kuma lissafin yadda ake kaso-kason wawuson damin Hauron Haurobiya a hannun Uwargida In-gwangwaje-in-wala yake. To don me ‘Santalla ba za ta sakata, ta wala ba?’ Kai kowa ya samu rana sai ya yi shanya.
’yan makaranta, na kattaba muku wannan makala ne, a darassinmu na wannan mako, don jan na-zomonku, kan lallai ku kyale Santala ta wataya, ta yadda na-mujiyarku zai sha kallo. Idan kuka kyale Santala, za ta nuna muku cewa alkafurar Tsuntsun Danniya ai wasan ‘’yan dugwi-dugwi ne kawai; Shamuwar Somaliya da Belbelar Bi’u na zamanin Farfesun Borin-shorido ba su iya komai ba, wajen salwantar da rayuka da dukiyoyin al’umma. Tunda Shugaba Jatau Mai-sa-in-sa da Dauda-mai-maki da Tumbin-wulli sun ki tsawatar mata, sai in ce da Haurobiyawa, ‘a sha kallo cikin lumana.’ Ke kuwa Santala ki ci aba da gashi, suya sai ranar salla! Maganin alkafura da wuntsula gudi-gudin tsuntsaye a sararin samaniyar Haurobiya, ta yiwu Gwamnati ta gano duk masu cin kwaiduwa ba za su fada cikin wannan hadari ba; ko kuma Majalisar Haurobiya ta amince da hujjar Santala cewa Mai-duka ne ke haifar da hadurra tsuntsayen sama, koda kuwa an yi gangajin kula da rubabbun na’urori; ko an yi kwashi kwaraf da Hauron al’umma, an sayo musu rubabbun tsuntsaye wadanda ba su da nagarta. Ni dai ba ni na fada ba. Masu hankali a hannun riga sai ku ci gaba da mara wa Santaleliyar kwaiduwa baya, don ta kara ingata ayyukanta na kassara duk tsunsun da ya keta sararin samaniyar Haurobiya. Ba sai na yi faskaren ma’anoni ba, kowa ya fasko cewa, Santala ta yi wa Araruma da ’Yardidi Fintikau, wajen raruke lalitar kasar Haurbiya.
Sakon makaranta
Na ’yanta dalibai
Mai alfarma Shugaban Sunduki, kuma bakon Dube-Dube, bakin Balarabe, jikan Abu Zayd ya ’yanta dukkan daliban makarantar nan ta dodanni da ba a gamata. Kuma dlaiban ba su zama dodanni. Shedaniyar makarantar da bata yaye dalibanta. Duk ku watse na ‘yanta ku. Tsarabar ku ke nan daga Dubai. Daga Shehin Sunduki, Bayan Otal din Ci-da-kanka, Haurubja Babban Birnin Haurobiya. 08039686854