Shahararren dan kwallon Najeriya Super Eagles Sani Kaita a karshen makon jiya ne ya koma kasar Turai bayan ya gama kwantaragin wata uku a matsayin aro a kulob din Enyimba na Aba.
Ya koma kasar Moldoba ce kasar da ke kusa da Rasha inda zai cigaba da yi wa kulob din FC Sadan Ceadir Lunga wasa.
dan kimanin shekara 28, Sani Kaita ya dawo Najeriya ne don ya yi wasa a gasar rukuni-rukunin Najeriya tun bayan da Hukumar shirya kwallon kafa ta kasa NFF ta bullo da shirin ba ’yan Najeriya da ke wasa a kasashen ketare damar komawa gida don sanya hannu na wucin-gadi a kungiyoyin kwallon kafa da ke fafatawa a gasar ta firimiya a duk lokacin da suka samu hutu.
Ya buga kwallo a wasan da Enyimba ta yi da kungiyar kwallon kafa ta Sharks da ke Fatakwal inda aka tashi 1-1 kafin ya jefa kwallon da ta ba Enyimba nasara a wasan da ta yi da kulob din Kaduna United a wasa na 13 a gasar ta Firimiya inda aka tashi da ci 1-0.
Sani Kaita ya koma Turai bayan gama kwantaraginsa a Enyimba
Shahararren dan kwallon Najeriya Super Eagles Sani Kaita a karshen makon jiya ne ya koma kasar Turai bayan ya gama kwantaragin wata uku a matsayin…