✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Sanchez ba zai buga wasan Arsenal na yau ba

Kocin Arsenal, Arsene Wenger ya ce xaya daga cikin ’yan kwallonsa Alexis Sanchez ba zai buga wasan firimiyar da kungiyarsa za ta yi da ta…

Kocin Arsenal, Arsene Wenger ya ce xaya daga cikin ’yan kwallonsa Alexis Sanchez ba zai buga wasan firimiyar da kungiyarsa za ta yi da ta Leicester City a yau Juma’a ba.

Alexis Sanchez wanda yake yunkurin barin kulob xin, sai a karshen makon jiya ne ya koma kulob xin bayan dogon hutun da ya yi tun bayan da aka kammala kakar wasan da ta wuce.

Kamar yadda kocin ya nuna, ya ce xan kwallon ba zai buga wasansu na yau ba ne saboda matsalar ciwon ciki da take damunsa.  Haka kuma ana sa ran ba zai buga wasan da kulob xin zai yi da na Stoke City a makon gobe ba, duk saboda matsalar ciwon cikin. 

Masana harkar kwallo sun ce kimanin shekaru 4 kenan a jere da ake doke kulob xin Arsenal a wasannin farko da take yi a gasar fimiriyar Ingila kuma alamu sun nuna a wannan karon ma ba za ta sake zane ba.

Alexis Sanchez dai ya yi duk mai yiwuwar ganin ya bar kulob xin Arsenal a kakar wasa ta bana amma hakan bai yiwu ba, al’amarin da ake ganin zai hakura ya zauna har sai bayan kwantaraginsa ta kare a kakar wasa ta bana kafin ya samu damar canza shekar.