✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Sanatan Kano ya dauki nauyin karatun dalibai 100 a fannin lafiya

Sanatan Kano ta Kudu Suleiman Abdulrahman Kawu ya dauki nauyin dalibai 100 daga mazabarsa su karanci fannin kiwo lafiya

Sanatan Kano ta Kudu Suleiman Abdulrahman Kawu ya dauki nauyin dalibai 100 daga mazabarsa domin su yi karatu a fannin kiwo lafiya a kan Naira miliyan 153.

Dalibai mata 40 da maza 60 da Sanata Kawu Sumaila ya dauki nauyin nasu daga kananan hukumo 16 da ke mazabarsa, za su yi karatu ne a fannin aikin jinya da dangoginsa.

Abin da ya biya ya hada da kudin rajista, na dakin kwana da sauransu, sai kuma alawus din Naira 10,000 ga kowane dalibi a duk wata na tsawon shekara daya.

Makarantun da daliban za su yi karatu su ne Aminu Dabo College of Nursing Science, Pyramid College of Nursing, Rawafiq International College, Dansharif College of Nursing da kuma Iqra’a College of Nursing.

Da yake magana a taron kaddamar da daliban, Sanata Kawu Sumaila ya ce zai biya kudin daukar nauyin rukuni na biyu na karin dalibai 100 a watan Janairun 2024, sannan akwai rukuni na uku da zai biyo baya.

Ya ce hakan yana daga cikin alkawuran zaben da ya yi, kuma burinsa shi ne kafin karewar wa’adinsa, ya samar da jami’an lafiya akalla 200 da za su kula da cibiyoyin lafiyar mazabar da ke fama da karancin ma’aikata.

“Zuwa lokacin da za a yaye rukuni na uku, cibiyoyin lafiya da muke da su za su samu isassun ma’aikata,” in ji shi.

Wata daliba da ta ci gajiyar tallafin, Aisha Abubakar ta bayyana cewa ya ba ta damar cimma burinta na zama ma’akaciyar lafiya.