✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Sanata Sikiru Osinowo ya riga mu gidan gaskiya

Sanata mai wakiltar Legas ta Tsakiya a Majalisar Dattawa Sanata Sikiru Osinowo ya riga mu gidan gaskiya. Sanata Sikiru Osinowo wanda aka fi sandi da…

Sanata mai wakiltar Legas ta Tsakiya a Majalisar Dattawa Sanata Sikiru Osinowo ya riga mu gidan gaskiya.

Sanata Sikiru Osinowo wanda aka fi sandi da Pepperito ya rasu ne a asibiti sakamakon rashin lafiya.

Kakakin Jam’iyyar APC na jihar Legas, Hon. Seye Oladejo ya tabbatar da rasuwar dan majalisar.

Mamacin ya rasu yana da shekaru 65. Kafin rasuwarsa ya yi dan Majalisar Dokokin Jihar Legas mai wakiltar mazabar Kosofe daga 2003 zuwa 2019.

Daga nan ya zama dan Majalisar Dattawa mai wakiltar Legas ta Tsaksiya har zuwa lokacin rasuwarsa.

Marigayi Sanata Osinowo na da cikin na gaban goshin jigon jam’iyyar APC Bola Ahmed Tinubu.