Allah Ya yi wa Tsohon Sanatan Kaduna ta tsakiya, Sanata Ahmed Aruwa rasuwa da safiyar yau Lahadi.
Aruwa ya rasu da misalin karfe 4:30 na asubah a wani asibiti mai zaman kansa da ke unguwar Barnawa a jihar Kaduna.
Dan uwan Aruwa, Suleiman Kuta ne ya tabbatar wa majiyarmu rasuwar tsohon Sanatan.
Aruwa wanda ya wakilci Kaduna ta tsakiya a majalisar dattawa tsakanin 1999 zuwa 2007, ya rasu ne bayan doguwar jinya.
Allah ya ji kansa da rahama, Amin.