Gwamnatin Jihar Kano ta bayar da sanarwar tube Mai martaba Sarkin Kano Malam Muhammadu Sanusi II daga gadon sarauta bisa zarginsa da rashin biyayya ga ofishin Gwamnan Jihar da sauran ma’aikatun jihar.
Da yake bayar da sanarwar tube Sarkin, Sakataren Gwamnatin Jihar, Alhaji Usman Alhaji ya ce, Majalisar Zartarwar Jihar Kano a karkashin jagorancin Gwamna Abdullahi Umar Ganduje, ta tube Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II ne daga sarauta saboda abin da ya aikata ya saba wa sashi na A zuwa E na kundin dokokin Jihar Kano.
A cewar Sakataren Gwamnatin “Sarkin Kano ya nuna rashin biyayya ga Gwamnan Jihar Kano da kuma kin bin dokokin jihar. Hakan ya jawo gwamnati ta dauki matakin tube shi bayan ta tattauna da masu ruwa-da-tsaki.”
Ya bayyana cewa, za a bayar da sanarwar sabon Sarkin Kano zuwa wani lokaci a nan gaba.
Ya yi kira ga jama’ar jihar kowa ya ci gaba da harkokinsa kamar yadda aka saba.
A safiyar ranar Litinin din nan an samu kai ruwa rana a tsakanin wakilan Majalisar Dokokin Jihar Kano a kan rigimar da ke tsakanin Gwamnatin Kano da Sarkin Kano.
Rigimar ta fara ne bayan da Shugaban Kwamitin Sauraron Korafe-Korafen na Majalisar Alhaji Hamza Rabi’u, ya yi bayanin abin da ya gano game da korafe- korafe biyu da aka yi a kan Sarkin, wanda hakan ya jawo wasu wakilan majalisar musamman na bangaren Jam’iyyar PDP suka kalubalance shi cewa, abin da ya yi ya saba da dokar gidan cewa idan majalisar tana zama ba a yin magana a kan wani korafi da ke gaban wani kwamitin da bai mika rahotonsa ga majalisar ba.
Hakan ya jawo wakilan majalisar da suka fito daga jam’iyyun APC da PDP suka fara fada da juna don dauke sandar majalisar inda a karshe jami’an tsaro suka yi nasarar dauke sandar majalisar.
Tun bayan da aka kammala zaven bara aka fara samun rikicia tsakanin Gwamnatin Jihar Kano da Sarkin Kano, inda gwamnatin ta kirkiro sababbin masarautu hudu a jihar.