Neman kudi ko dogaro da kai abu ne mai matukar amfani da tasiri ga rayuwar mutum.
A lokuta da dama, wasu sun fi mayar da hankali kan neman kudi, ma’ana su dogara da kansu maimakon tsayawa neman aikin gwamnati ko aiki a karkashin wani.
- Tsakanin Kwankwaso da Obi wani zai mara min baya — Atiku
- Hadimar Gwamnan Sakkwato ta rasu sakamakon turmutsutsu a taron PDP
Wannan ta sa Aminiya ta zakulo muku wasu sana’o’i biyar da za ku iya fara da kudi Naira 150,000.
Wadannan sana’o’i su ne kamar haka:
1. Wankin mota: Wankin mota sana’a ce da take da rufin asiri sosai kuma masu mota kan kai wankin motarsu a lokuta da sama maimakon tsayawa su wanke da kansu.
A wasu jihohi irin su Kano, Kaduna, Jigawa, akan wanke wa mutum mota a Naira 500, 1,000 da kuma 1,500, yayin da a wasu jihohin ma ana wanke wa har zuwa 2,000, ko sama da haka.
Da zarar mutum ya samu kayan aiki da kuma wurin da zai fara sana’ar, ba abu ne mai wahala ba wajen samun masu kawo masa wankin.
2. Kitso da kwalliya: Wannan sana’a ta jibanci mata ne musamman a kabilar Hausawa, amma wasu kabilun akan samu maza na yin sana’ar kitso da kwalliya.
Sana’a ce da ba ta bukatar wani jari mai yawa, idan kitso ne hannun mutum shi ne jarinsa. Idan kuwa kwalliya ce, kayan kwalliyar da mace za ta saya ta fara sana’arta a gida ba za ta kashe sama da dubu 100 ba.
Daga cikin kayan kwalliyar da za ta saya akwai tarihin burushin da ake kwalliya, hoda iri daban-daban, mayukan shafawa da sauransu.
3. Sana’ar PoS: A yanzu harkar cire kudi da turawa ta hannun masu sana’ar PoS ya saukaka wahalhalun zuwa banki. Kazalika sana’ar ta samar wa da matasa masu yawan gaske abin yi.
Mutum ya kan ita fara wannan sana’a da mafi karancin kudi Naira dubu 100. A sannu-sannu wata rana jarinsa zai bunkasa.
4. Kasuwanci a Intanet: Fasahar zamani ta bijiro da dabarun kasuwanci a wannan karni da muke ciki. Mutane da dama su kan fara saye da sayar da kayayyaki a Intanet.
A lokuta da dama wasu kan fara kasuwanci a Intanet da dan karamin jari, ta hanyar sayen abu su dora a Intanet idan mai so ya gani ya saya.
A haka wasu suke bunkasa har su bude manyan shaguna, irin wannan an same su masu tarin yawa da suka fara kasuwancinsu a Intanet.
5. Gyaran waya: Wannan sana’a ce ta dogaro da kai mai matukar tasiri duba da yadda waya ta zamo wani sashe na rayuwar al’umma a yanzu. Abin da mutum ke bukata kafin fara wannan sana’a shi ne ilimin gyaran waya.
Sai kuma kayan gyaran da zai ke yin aiki da su wadanda baki daya ba za su wuce dubu 100 ba baki daya.
Wadannan su ne kadan daga cikin sana’o’in hannu da Aminiya ta zakulo domin fadakar da masu karatu kan muhimmancin neman na kai, Hausawa na cewa ‘Mai nema, yana tare da samu’.