✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Sana’ar Tattara Kwalaye na kara daraja – Auwalu Dala

Me ya jawo hankalinka ka rungumi sana’ar tattara kwalaye maimakon a baya da aka fi saninka da sana’ar sayen karafa? To ita dai sana’a yawanci…

Me ya jawo hankalinka ka rungumi sana’ar tattara kwalaye maimakon a baya da aka fi saninka da sana’ar sayen karafa?

To ita dai sana’a yawanci ana yinta ne saboda a samu a rufa wa kai asiri, harka ce wadda an dade ana yinta amma sai a kwanan nan ta shigo nan Kalaba. Kuma mutane suna amfana da harkar kuma tana taimakawa wajen rage datti a gari, tun da abin da za a zubar da shi ya zama bola, ya kawo cunkoso, yanzu ya zama za a diba a fitar da shi, a sake sarrafa shi zuwa wani abin amfani.

Ina kuke kai kwalayen kuna sayarwa?

Muna kai shi Legas da Benin da kuma Kano.

Su masu saye daga wurinku, me suke yi da shi?

Suna sarrafa shi, a yi maganin sauro da kiret din da ake sanya kwai da kuma wasu abubuwa na amfanin mutane kuma harkar tana taimakawa sosai.

Yaya batun farashin saye da sayarwa a wannan harka?

E, muna sayen ko wane kilo kan Naira 20 a hannun wadanda suke kawo mana, wasu kuma ’yan sari suna dora Naira 5, su sayar Naira 25 zuwa Naira 30.

Alhamdu lillahi ba laifi, tun da ita sana’a komai kankantarta idan mutum yana yi, Allah Ya sanya mata albarka sai ya gode masa.

Wannan sana’ar ko tana bukatar wani isasshen jari kafin mutum ya fara?

Ita gaskiya ba ta kai kamar karfe jan kudi ba. Misali, idan a nan Kalaba ne za ka gudanar da sana’ar, wato ka rika sayarwa, Naira dubu 70 ko 100 za ta ishe ka. Idan kuma za ka tura shi zuwa Legas ne sai ka tanadi akalla Naira dubu 500 zuwa 600.

Wane kalubale kuke fuskanta a wannan sana’a?

Babu, sai dai kawai farashinsa yana tashi kamar yadda na karfe yake a yanzu.

Wane buri kake da shi game da wannan sana’a?

Burina shi ne in ga kwali ya yi farashi kamar yadda karfe yake da shi a yanzu, kamar yadda ake sayensa, shi ma kwali a saya haka.

Ko akwai wani bayani da za ka yi ga jama’a, a game da wannan sana’a?

Abin da zan gaya wa mutane shi ne, ita sana’a wanda ba shi da ita zai zama koma baya cikin jama’a, yadda ba zai iya taimaka wa kansa ba bare wani. Duk wani wanda ka ga ya samu daukaka ta hanyar sana’a ce har shi ma ya zama wani ake labarinsa. Da sana’a ce za ka iya taimakon kanka har ma ka taimaki wani. Hatta matsalolin da muka samu na tsaro, da a ce mutane suna da sana’ar yi ko ayyukan yi, ba za a samu irin wadannan matsaloli ba.