✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Sana’ar gwangwan ba sata ba ce – Alhasan Gezawa

Wani matashi wanda sana’ar gwangwan ke yi da da shi a Jihar Ogun ya shaida wa Aminiya cewa, abin takaici ne yadda jama’a ke yi…

Wani matashi wanda sana’ar gwangwan ke yi da da shi a Jihar Ogun ya shaida wa Aminiya cewa, abin takaici ne yadda jama’a ke yi wa masu sana’ar gwangwan kallon barayi bayan kuwa su ma a zahiri saye da sayarwa suke yi kamar sauran ‘yan kasuwa. 

Matashin mai suna Alhasan Muhammad Hassan Gezawa ya ce mutane da yawa sun yi wa sana’ar gwangwan mummunar fahimta, duk da kasancewarta sana’a ce mai rufin asiri da tsaftace gari da ma uwa uba samar wa matasa ayyukan yi. “
“A karamar Hukumar Gezawar ta Jihar Kano aka haife ni, a nan na yi karatun Firamare da na sakandare, baya ga na addini daga nan ban samu ikon cigaba da karatu ba, saboda wasu dalilai sai na ga ya dace in nemi sana’ar dogaro da kai. Nan na yi shawara da wani ɗan uwana da ake kiransa Maidukiya, wanda yake zuwa Jihar Ogun ya amince da buƙata ta, muka taho da shi nan Abekuta aka hada ni da mai gidana, wanda a lokacin yake ba ni Naira dubu uku duk safiya in rataya buhu in shiga gari neman kayan gwangwan. Kuma a yanzu sai godiya, domin kuwa na shiga sana’ar da kafar dama, don har na kai ga malakkar rumfa, sannan akwai akalla mutum 50 da ke karkashina a wannan rumfa, duk safiya suna zuwa na ba su jari su shiga gari neman kaya” inji shi.
Malam Alhassan ya kara da cewa, babban abin da yake ci masa tuwo a kwarya shi ne yadda mutane ke yi wa ‘yan gwangwan kallon barayi ,bayan duk wani dan gwangwan da ka gani ya saba buhu ya fita nema yana da mai gidan sa da yake ba shi jarin kudin sayen kaya.
“Kullum safiya sai iyayen gidan sun yi wa yaran su kashedi da su guji kayan sata, sannan kada su ga wani abu su dauka, sai dai su saya. A haka ne za ka ga yawancin mukan sayi karafunan mota ne daga makanikai da kuma daidaikun jama’a, domin ita sana’ar gwangwan ko bola jari sana’a ce da a yanzu ta cigaba, ta wuce yadda ake zato, domin ba karafa da alminiyon kawai muke saye ba, hatta ga ledar ruwa ta fiya wata da buhuhuna da kwalaye da kasusuwan saniya. Muna saye mu kai kamfani, musayar su kuma su sarrafa su zuwa abubuwa daban-daban” inji shi.
A cewar Malam Alhasan baya ga dimbin guraben ayyukan yi da sana’ar ke samarwa tana kuma tsaftace gari, ta hanyar kawar da karafa da ledoji da sauran buraguzai daga kan hanyoyi, sannan sana’a ce da suke yin ta kai tsaye da masana’antu, wadanda suke ba su makudan kudi su nemar musu kaya da su. Don haka sana’a ce da ke bukatar gaskiya da rikon amana. Domin sai mutum ya zamo mai gaskiya da amana sannan ne zai samu cigaba a sana’ar.
Malam Alhasan Ya shaida wa Aminiya cewa, babban kalubalen da ya taba fuskanta a sana’ar gwangwan shi ne a wani lokaci can a baya ya taba sayen wasu karafa a kan kudin da bai wuce Naira 300 ba, amma sai da takai ya yi asarar fiye da Naira dubu 300.
“Kasan mu ‘yan gwangwan lalatattun kayayyaki muke sayensu a banza mu kuma sayar da su a banza, sai bayan da na sayar da kayan sannan aka ce ai karafa ne masu daraja a haka na yi ta fama na tafka asara. Sai dai alhamdulillahi, domin na afana kwarai a wannan sana’a baya ga kimanin mutum 50 da suke samu a karkashina, ni ke daukar nauyin karatun kannena da dawainiyar iyaye na da ‘yan uwana, kana na kai ga gina gidaje na biyu; sannan ina da motar hawa. Don haka duk mai neman rufin asiri a wannan sana’a in ya shige ta bisa gaskiya da rikon amana sai ya samu cigaba.
A karshe Malam Alhassan ya yi kira ga gwamnati da ta dinga kulawa da masu sana’ar ta gwangwan, bisa la’akari da irin gudunmawar da suke bayar wa. Domin a yanzu ba sa amfana ta ko’ina, in ban da yadda aka mayar da su tamkar wata saniyar tatsar jami’an tsaro .