✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Sana’a ta kai Bahaushe Kurmi ba leburanci ba –Sarkin Hausawan Ibadan

Mai martaba Sarkin Hausawan Ibadan, Dokta Ahmad Ɗahiru Zungeru ya bayanna cewa Hausawa mutane ne da aka san su da kasuwanci da neman na kansu…

Mai martaba Sarkin Hausawan Ibadan, Dokta Ahmad Ɗahiru Zungeru ya bayanna cewa Hausawa mutane ne da aka san su da kasuwanci da neman na kansu tun gabanin zuwan Turawa. Ya ce maula da tumasanci ba halin da aka san Bahaushe da su ba ne. Tun gabanin zuwan Turawa Hausawa suke zuwa garuruwan Kurmi da Ghana, wato Gwanja domin kasuwanci.

Sarkin Hausawan ya yi wannan tsokaci ne a yayin bikin cikarsa shekara 25 bisa karagar mulki, wanda ya gudana a ranar Asabar ɗin da ta gabata a Unguwar Sabo-Ibadan da ke babban birnin Jihar Oyo.

Kamar yadda ya ce, a wancan lokacin, mutumin da ya fara yada zango, ya zauna tare da iyalinsa shi ne ake kira da Nagarke, ɗan kasuwa ne shi Bakano. “Shi ne kuma Sarkin Fawa, wanda ya yi harkokin kasuwancinsa a Kano da Sakkwato, sannan ya zo nan garin Ibadan ya zauna. Attajirin ɗan kasuwa ne, a lokacin ma babu Sarkin Ibadan na Yarabawa sai mai unguwa. Tun a wannan lokacin su Hausawa suna zuwa cinikin goro ne har suka fara kawo shanu,” inji shi.

Ya kara da cewa: “A nan ne suka wayar wa da Yarabawa kai a harkar kasuwancin shanu. Da lokaci ya yi Hausawa suka yi yawa, bayan an gano goro a garin Ibadan, inda suka yada zango, sai wani rikici ya taso. Yarabawa suka ce ba su yarda Hausawa su dinga shiga daji suna sayo goro ba, sai dai su Yarabawan su sayo a saya a hannunsu. Da lokaci ya yi, Turawan mulkin mallaka suka faɗa wa shugabannin Yarabawa cewa lokaci ya yi da ya kamata a bai wa Hausawa wurin zamansu na kansu, tun da sun yi yawa.

“To, wannan shi ne musabbabin da ya sa aka bai wa Hausawa unguwar Sabo-Ibadan a shekarar 1893. Wannan unguwa ita ce Sabo ta farko a Najeriya, sannan sai Sabon Gari ta Kano. Don haka muke daɗa faɗakarwa domin a sani cewa Bahaushe ba leburanci ya kawo shi Kurmi ba, da jarinsa ya zo da kuma kasuwancinsa ya zo.”

A nasa jawabin, Galadiman Katsina Mai Shari’a Mamman Nasir ya yi kira ga ’yan Najeriya da su kasance masu son zaman lafiya. Ya ce babu wani abu da zai ba da ma’ana matuƙar babu zaman lafiya, domin zaman lafiya shi ne ginshiƙin ci gaban kowace al’umma. “Don haka aikin da muka sanya a gaba ke nan, yaya za a zauna lafiya? Na halarci taro a Jihar Benuwai, a ƙarƙarshin inuwar Gidauniyar Tunawa da Sa Ahmadu Bello Sardaunan Sakkwato. A wannan zama da muka yi, mun sasanta rikici a tsakanin tsohon gwamnan jihar da gwamna mai ci a yanzu, baya ga tattaunawa da muka yi a kan rikicin Fulani makiyaya da na manoma; inda suka bayyana mana cewa wannan rikici na baya-bayan nan ba irin rikicin da aka saba gani tsakanin Fulani makiyaya da manoma ba ne. Yanzu haka za mu je Jihar Taraba, inda nan ma za mu duba yadda za mu lalubo bakin zaren. Fatanmu shi ne samun zaman lafiya,” inji Galadiman Katsina.

A yayin bikin, masarautar ta Sarkin Hausawan Ibadan ta yi karin naɗin sabbin ’yan majalisarta, ta kuma karrama wasu mutane da suka yi fice wajen ba da gudunmawarsu ga ci gaban ƙasa. Cikin wadanda aka nada har da tsohon Sufeto-Janar na ’yan sanda, Cif Mike Okiro da shugaban tashar Rediyon Liberty, Dokta Tijjani Ramalan.

Sarkin Hausawan na Ibadan ya jaddada muhimmacin zaman lafiya, ya kuma bayyana damuwarsa ƙwarai bisa rikice-rikicen da ake dangantawa da Fulani makiyaya, inda ya ce za su ci gaba da yin aiki tuƙuru domin tabbatuwar zaman lafiya.

Bikin ya sami halartar mai girma Galadiman Katsina, Mai Shari’a Mammam Nasir da sauran manyan baƙi daga sassa daban-daban na ƙasar nan tare da hakiman masarautar da sarakunan Hausawan wasu daga cikin jihohin Kurmi da Sarkin Sasa Sardaunan Yamma Alhaji Haruna Mai Yasin da wakilan tsohon Sufeto-Janar Mike Okiro.

A cewar Dokta Bayo, wanda ya wakilci Cif Mike Okiro, taron ya yi matuƙar ba shi sha’awa ganin yadda ya haɗa ɗaukacin ƙabilun ƙasar nan. “Wannan shi ne zai tabbatar maka da cewa kan al’ummar ƙasar nan a haɗe yake. Wannan abin sha’awa ne da ya kamata a yi koyi da shi,” inji shi.