Talatu Muncha mace ce mai kamar maza, wadda ke sana’ar kafinta a garin Lafiya na Jihar Nasarawa. A wannan tattaunawar da Aminiya, ta yi bayani game da kalubalen da nasarori da ta samu albarkacin sana’ar. Ga yadda hirar ta kasance:
Aminiya: Me ya ba ki sha’awar shiga wannan sana’a?
Talatu: Da farko dai zan so na fara da bayyana maka takaitaccen tarihina. Ni ce kadai iyayena suka aifa. Mahaifina ya rasu tun ina karama. Tun daga wancan lokaci wani kawuna ne ya ci gaba da daukar nauyin karatuna har na kammala sakandare. Daga nan dai ban samu damar ci gaba da karatuna ba sakamakon rashin kudi.
Wannan ya sa na gaya kawuna cewa ya nemi mini sana’a don in taimaka wa rayuwata, sai ya hada ni da wani abokinsa da ke aiki da Hukumar samar da aikin yi da ke nan garin Lafiya, inda na fara koyon wannan sana’ar kafinta. Ni da wasu ’yan mata biyu muka fara koyon sana’ar da farko. Amma daga baya sai wadannan ’yan mata suka janye don a cewarsu aikin na maza ne da ke bukatar karfi.
Ba shakka aikin kamar yadda ka sani na karfi ne da ba kowace mace ce za ta iya jure wahalar ba, don ni kaina zan iya tuna wa da na fara sana’ar sai da na yi rashin lafiya na wasu kwanaki, inda na yi tunanin dakatawa da sana’ar. Amma da na sake tunani mai zurfi, sai na ci gaba.
Bayan wasu lokuta sai hukumar ta hada ni da wani mutum don ya ci gaba da koya mini sana’ar. Amma ban samu kwarin gwiwa ba daga gurinsa. Wannan ya sa daga baya na bar wajen na koma, inda nake yanzu ina ci gaba da sana’ar. Kuma maigidana a nan ya dauki lokacinsa ya koya mini sana’ar sosai wanda da ikon Allah yanzu na kware a sana’ar don a yanzu nasan kusan dukka abubuwa da ya kamata na sani a sana’ar.
Aminiya: Me ’yan uwa da abokan arziki ke fadi game da sana’ar?
Talatu: Mahaifiyata da wasu ’yan uwana suna murna sosai da wannan sana’ata don sau da yawa za ka ji suna yaba mini cewa nasan muhimmancin dogaro da kai. Amma wasu daga cikin kawayena sukan yi mini dariya ka ji suna cewa wai ina ba ta lokacina ne kawai ya kamata na je, na yi aure ko na nemi wata sana’a daban kasancewa wannan sana’a ta kafinta maza aka fi sani da ita.
Aminiya: Me kike cewa wadannan mutane da basason ki da sana’ar?
Talatu: Nakan gaya musu cewa ina jin dadin sana’ar don ina ganinta a matsayin wata hanya ce ta atisaye. Kuma a koyaushe ina kasance cikin farin ciki da annashuwa don ina iya kera kushin na falo da akwatuna da kujeru iri daban-daban da kuma bugun kwanon gida da dai sauransu. Kuma ta wannan sana’a ce nake biyawa kaina bukatun rayuwa.
Aminiya: Ya ya kike hulda da abokan cinikayya a matsayinki na ’ya mace?
Talatu: Babu shakka a duk wurin da na tafi aiki za ka ga mutane suna so na, suna kuma yaba mini saboda sana’ata. Haka kuma saudayawa a duk lokacin da ni da maigidana muka tafi aiki a waje za ka ga abokan huldawanmu suna yaba wa aikina.
Kuma sanadiyana za ka ga suna ci gaba da kiranmu mu je mu yi musu aiki. Wadannan mutane za ka ji suna cewa ya yi kyau da nake amfani da damar da na samu wajen neman na kaina.
Aminiya: Wace shawara kike da ita ga ’yan uwanki mata?
Talatu: Shawarar da zan bai wa ’yan uwana mata ita ce su kama sana’a. Idan ba za su iya irin wannan sana’armu ta kafinta ba, akwai wasu sana’o’i daban-daban.. Koda kina aikin gwamnati, ki kama sana’a. Saboda na lura cewa sana’a ce kawai take hana maza wulakanta mace.