✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Samun man fetur a Arewa babbar nasara ce

Duk abin da ya kamata ku sani kan danyen mai a Arewa maso Gabas, yadda ake neman danyen mai da hakowa har a ci moriyarsa

Na san ko ba duka ba, amma akasarin ’yan Arewa sun shiga murna da farin ciki game da samun man fetur da aka yi a Kolmani, wani kauye da ke iyakar Jihar Gombe da wani bangare na Jihar Bauchi.

Ko da yake wasu lauyoyi Jihar Gombe sun fara kananan maganganu cewa yankin da aka samu man a jiharsu yake, bai shiga kauyen Barambu a Karamar Hukumar Alkaleri ta Jihar Bauchi ba.

Har ma sun yi barazanar shiga kotu don neman fassarar inda iyakokin jihohin biyu suka tsaya, domin tabbatar da ko Jihar Bauchi na da rabo a cikin wannan arzikin kasa da aka samu.

Ko da yake yanzu ba a kan wannan batu nake son yin sharhi ba.

Amma dai abu ne da ya kamata a duba shi da kyau, kuma a dauki matakin warware shi tun da wuri, domin kuwa yana iya zama kalubale mai girma nan gaba.

Sai dai kuma abin takaicin shi ne mu a Najeriya ba a cika daukar abu da muhimmanci ba, musamman a lokacin da yake farko-farkonsa, sai ya ta’azzara har ya fara zama alakakai sannan a fara daga hankali ana tunanin yadda za a shawo kansa. Kaico!

A cikin jawabin da Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ranar 22 ga watan Nuwamba, 2022, lokacin kaddamar da fara aikin hakar mai a wannan yanki na Arewa maso Gabashin Najeriya, ya bayyana cewa, duk da kalubalen tsaro da kasar ke fuskanta, da yadda farashin man fetur ke hawa da sauka a kasuwar duniya, Najeriya ta samu Dalar Amurka biliyan uku, da wasu kamfanonin kasashen waje suka saka a aikin hako man a Arewa, abin da ya ce ba karamin abin a yaba ba ne ga wannan gwamnati mai ci.

Babu shakka kamar yadda ya fada abin jinjina ne sosai, kuma ya kamata Arewa da al’ummarta su yi da gaske wajen tabbatar da ganin sun kare wannan arzikin da Allah Ya tabbatar musu da shi, bayan tsawon lokaci ana ta kwan-gaba-kwan-baya a kan za a samu man ko ba za a samu ba.

Har wani izgili ’yan Kudu suke yi musu bisa tunanin aikin neman mai a Arewa huhulahu ne!

Amma daga lokacin a can shekarun baya, da wata jarida a Kudu, Daily Times, ta buga a kanunta cewa, ‘The Mallams are coming!’ wato ’yan Arewa na tafe – Ya tabbatar da cewa hasashen zai iya zama gaskiya.

Alhamdulillahi, aikin hakar mai a Arewa ya tabbata, sakamakon jajircewa, kishin ci gaban Arewa, da aiki tukuru da aka yi, bayan biliyoyin Naira da aka kashe kan wannan aiki.

Fadi-tashin hako man Arewa

Wasu ’yan Arewa da dama ma ba su san fadi-tashin da ake yi ba, sai labarin fara aiki kawai suka ji.

Shi ma din, sai ya gamu da halin mu na ’yan Najeriya, inda aka rika izgili da abin ana masa kallon tatsuniya ce!

Abin da ba su sani ba shi ne kansu suke kwancewa zani a kasuwa.

Ko babu komai dai gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari ta cancanci a yaba mata, saboda hobbasan da ta nuna wajen tabbatar da ganin wannan mafarki da aka dade ana yi wa Arewa ya tabbata, duk kuwa da kalubalen da aka rika fuskanta game da aikin.

Arewa maso Gabas da Arewa ta Tsakiya sun zama yankuna masu samar da danyen mai, kashin bayan samar wa Najeriya kudaden shiga, don tafiyar da manyan ayyuka da muhimman ayyukan gwamnati.

Daga yanzu za a kara ganin kima da darajar Arewa da ’yan  Arewa don sun daina zama wa sauran yankunan Najeriya kaska, ko cima zaune.

Domin sanin muhimmancin wannan aiki da tarihin gwagwarmayar da aka sha wajen neman inda za a samu man fetur a Arewa, na tattauna da wani masanin harkokin ma’adinan kasa da albarkatun man fetur, Malam Ibrahim Sabo, wanda ya fayyace min yadda abin yake.

Muhimmancin abin ya sa ni ganin ya kamata in dan yi bayanin su kadan, ko jama’a za su yaba da abubuwan da Gwamnatin Shugaba Buhari ta yi wa yankin Arewa a wannan bangaren.

Da wahala mai karatu ya fahimci hakikanin yadda man fetur ke samuwa, har a kai ga amfana da shi, ba tare da cikakkiyar shimfida a kan shi man fetur din ba, kama daga inda ake samun sa, matakan da ake bi don tabbatar da samuwarsa, da kuma yadda ake kaiwa ga amfana da shi.

Duk wadannan abubuwa, mai ra’ayin sanin harkar da ta shafi man fetur na bukatar sanin su, don guje wa molon ka wajen yin bayani.

Ina ake samun danyen mai?

Man fetur, daya ne daga cikin arzikin da Allah Ya yi wa bayinSa a doron kasa, wanda ake samun sa cikin wasu nau’ikan duwatsu da ake kira a turance ‘Sedimentary Rocks’.

Duk inda ka ji an samu man fetur a duniya to, daga wadannan nau’in duwatsun ne, ko ya zama shi man ya yi tafiya daga cikinsu zuwa ma’adanarsa da ake kira ‘Reservoir’ a turance.

Kuma akan samu wajen adanar tasa da ba a duwatsun da na yi bayanin su a baya ba, amma da matukar wuya, don ba su da yawa a duniya.

Bugu da kari, ba kowane irin nau’in dutsen ‘Sedimentary’ ne yake iya samar da man fetur ba.

Dole wanda zai iya samarwa ya zama yana dauke da wasu sinadarai wadanda asalinsu daga kananan halittu ne — ko dai na kananan dabbobi ko kuma tsirrai — masu dauke da sindarin Carbon da na Hydrogen, wadanda wasunsu da wahala ido ya iya ganin su ba tare da an hada da taimakon na’urar ‘microscope’, mai kara girman abubuwa, ba.

Yadda dutsen ke samuwa

Dutsen ‘Sedimentary’ na samuwa ne daga wasu duwatsun, sakamakon farfashewa da suke yi, sai kuma ruwa, iska ko kankara mai tafiya su dauke su daga inda suka farfashe zuwa inda za su ajiye su, idan karfinsu na tafiya ya ragu, ko ya kare.

Wannan waje da suke zuwa su jibge fasassun duwatsun su ake kira ‘Basin’ a turance, wato wata gaba ko rami da yake a waje mai gangara.

Akwai wata hanyar ta daban da ake samun duwatsun ‘Sedimentary,’ amma ba zai yiwu a kawo a wannan takaitaccen rubutu ba.

Yankunan da ke da dutsen

A Najeriya yankunan da suke da irin wannan ‘basin’ din da ke da tarin duwatsun ‘Sedimentary’ sun hada da Sakkwato, yankin Tafkin Chadi, Tudun Binuwai wanda ake kira Benue Trough, Bida a Jihar Neja, yankin Neja Delta da kuma bangaren Dahomey wanda ke yankin Jihar Legas.

Cikin wadannan gaba dayansu, yankin Neja Delta ne kawai ke samar da man fetur ga Najeriya a halin yanzu, sai kuma kalilan daga yankin Dahomey.

Yanzu kuma tafiya ta fara karasowa Arewa.

Yadda ake samun danyen mai

Bayan samuwar duwatsun ‘Sedimentary’ a waje, akwai wasu ka’idoji da dole sai an same su sannan a fara batun yiwuwar samun mai ko rashin yiwuwarsa.

Wadanan kuwa, sun hada da dutse mai samar da mai, dutse mai rumbun ajiyar mai, dutse mai rufe saman rumbun saboda hana ficewar man ko asarar sa, sai kuma tarkon da zai kame man a waje daya a cikin rumbun dutsen.

A baya na ambaci wasu sinadarai da ake bukata a dutse kafin ya zama wanda zai iya samar da mai.

To wannan dutsen idan aka yi dace bincike ya tabbatar cewa akwai wadannan sinadaran na Carbon da Hydrogen, daga kananan dabbobi ko kuma tsirrai, to za a dauke shi a matsayin wanda zai iya samar da danyen mai, wato ‘Source Rock’ a turance.

Hakan kuwa na yiwuwa ne kadai idan dusten ya binnu a can cikin kasa yadda zafin cikin kasar zai iya dafa shi ya matse shi da taimakon takurewar da kasar take yi.

Wannan dutsen a Najeriya shi ne ‘Shale’, amma akan iya samun wani nau’in dutsen ya bada haka a wasu yankunan na duniya.

A Neja Delta dutsen ‘Akata Shale’ shi ne ke samar da wannan man.

Wani dutsen da ke ba da makamashi na iya samar da man fetur, wani kuma iya iskar gas, wani kuma duka biyun.

Rumbun danyen mai

To, bayan wannan sai a samu wani dutsen da shi kuma aikinsa shi ne ya zama rumbun ajiyar man da zai fito daga dutsen da zafin karkashin kasa a dafa — wannan dutsen shi ake kira Rumbun Ajiyar Mai.

Shi ma kuma yana da wasu ka’idoji da sai sun cika zai iya wannan aiki.

Misali, na yankin Neja Delta shi ne Agbada, na yankin Gongola kuma a Arewa shi ne Dutsen Bima.

Dutsen karshe shi ne zai yi wa rumbun danen man rumfa saboda adana mai daga tafiya zuwa sararin kasa, wanda hakan zai iya sawa a yi asarar sa, ko kuma ya je ya hade da kasa a rasa wasu sinadaran; hakan sai ya sa idan aka yi rashin sa’a sai man ya zama ya wofinta.

To, bayan haka kuma a cikin rumbun  dole yanayi ya samu, wanda zai tattare man waje daya, ya zama kamar wata jakar ajiya a cikin rumbun.

Na san da yawan mutane suna tunanin mai a cikin kasa ne kamar yadda suke ganin rijiyar ruwa a gidajensu, to ba haka ba ne.

Tamkar dai ka ce ruwa ne da ke naso a cikin soson katifa, wanda ke fita a hankali, lokacin da takura ta ragu ko aka huda shi.

Cin moriyar danyen mai

Bayan mun san ka’idojin da ake bukata kafin a mayar da hankali a kowane waje don neman man fetur, yanzu kuma za mu yi duba zuwa ga matakan da ake bi har a kai ga cin moriyar man.

Karkashin haka akwai wasu matakai da za a iya kasa su gida uku; Na daya, matakin binciken alamomin samuwar mai.

Sai na biyu, na tabbatar da samuwar man da kuma matakin fitar da mai don amfani da shi.

Matakin bincike

A matakin farko ana amfani ne da ilimin binciken ma’adinan karkashin kasa, don nazartar yanayin wajen, daga kan duwatsu, samuwar rumbun ajiyar mai, yiwuwar samun jakar ajiyar man, har zuwa rumfar da za ta lullube wannan yanayin.

Daga nan sai wasu bincike da ake gudanarwa da ya shafi gutsuro dutsen da debo kasar wajen don gwajin dabi’arsa ta sinadarai, musamman inda aka samu yoyon mai daga rumbun ajiyar saboda hujewar rumfar da ta lullube wannan yanayin da ke samar da mai.

To dadi a kan haka, akwai wasu aune-aune da ake yi don a ga hoton cikin kasa, a samu karin karfin gwiwa kan wajen da man ke kwance, shi ma yana nan nau’i-nau’i, amma saboda takaitawa ba zan ambato su ba.

Tona rijiyar mai

Bayan samun nasara da karfin gwiwa a mataki na farko, abu na biyu shi ne tonon rijiya don tabbatar da samuwar abin da ake hasashe, domin gani ya kori ji.

Nan ne za a gani, shin akwai man? Mene ne yanayinsa? Yaya yawansa? Mene ne iyakarsa? Idan an fara debowa kwalliya za ta biya kudin sabulu ko bata lokaci za a yi? Sannan yaya kyan man? Yaya yanayin zafin karkashin kasar wajen yake? Mene ne karfin takurar wajen yake, don kauce wa karfin iska da ka iya fita ta haifar da asarar dukiya da rai?

Matakan tonon rijiyar mai

To, karkashin wannan ma akwai rijiyoyi da ake tono har matakai uku.

Da farko ana haka rijiyar bincike ta kintace, saboda babu tabbacin inda man yake.

Cikinta kawai so ake aga shin da man nan a kasa? Wanne iri ne? Yaya yanayin zafin wajen da takurarsa, wane zurfi ne zai kai ga rumbun ajiyar da sauran abubuwa da ake bukatar sani na bincike.

Sai kuma a kai ga rijiyar tantance yawan man, inda jakarsa take, da kuma sanin iyakarsa da kuma kididdige arzikin man bisa lura da kudin da za a kashe don debo shi, saboda kar ya zama asara ce za ta biyo baya.

Sannan akwai kuma rijiyoyi na karshe wadanda daga su ne ake fara debo man bayan an riga an san inda yake kwance.

Wannan rijiyar ce ta karshe a matakin neman danyen mai, daga ita sai cin moriyar doguwar wahala da aka yi, idan an dace da yawan man da kuma sauran ka’idojin.

Farkon hakar mai a Arewa maso Gabas

A harkar binciken neman man fetur da ake yi a wannan yanki na Arewa, a baya an tona rijiyoyin neman mai kimanin guda 23, a yankin Gabar Chadi ko ‘basin’ din Borno, amma iskar gas kawai aka samu.

Wannan bincike ya faru ne karkashin sashin kula da neman mai da a baya ke karkashin ma’aikatar NAPIMS na kamfanin NNPC a yanzu.

Farfesa Nuhu George Obaje, kwararre ne a bangaren nazarin yankuna masu yiwuwar samar da man fetur, ya bayyana cewa, rijaya ta farko da aka tona a yankin Tudun Binuwai (Benue Trough) wanda jihohin Bauchi da Gombe ke karkashinsa, kuma aka fi sani da karamin bezin din Gongola, ita ce rijiyar Rafin Kolmani ta daya, wacce kamfanin mai na Shell Nigeria Exploration and Production Company (SNEPCO) ya yi a shekarar 1999.

Zurfin rijiyar ya kai kimanin mita 3,000, amma ba a samu komai ba sai tarin iskar gas da ya kai dunkulen kafa biliyan 33 da kuma mai dan kadan.

Wannan ita ce kadai rijiyar da kamfanin na SNEPCO ya tona a yankin Gongola.

Sauran rijiyoyi biyu da aka tona a yankin sun hada da Kuzari ta farko da Nasara ta farko, wadanda kamfanin mai na Elf Petroleum Nigeria Limited (TotalFinaElf) ya tona, su ma a shekara ta 1999, masu zurfin kimanin mita 1,666.

Sai kuma wadda kamfanin mai na Chevron ya haka a shekara ta 2000 wadda zurfinta ya kai mita 1,500.

Sai dai duk wadannan rijiyoyi ba a yi nasarar samun wani abu na mai a cikinsu ba.

Amma masana a fannin neman albarkatun mai sun bayyana cewa ya kamata zurfin rijiyoyin ya fi haka, saboda za ta iya yiwuwa ba a kai inda man yake ba.

A cewarsa, sau tari dama sai an tarar da iskar gas, wacce ke zama kamar hula a saman mai sannan gaba da ita a samu man, ko kuma in babu, a rasa.

Saboda taimakon sabbin fasahar zamani na gudanar da binciken neman mai irin su 3D seismic wato hoton karkashin kasa da ake samarwa ta hanyar amfani da gudun kara don bambance yanayin abubuwan da ke karkashin kasa (kamar dutse, iska da ruwa), da wasu fasahohin kuma, sai a shekarar 2019 ne Shugaban Kasa Muhammadu Buhari a ranar 2 ga watan Fabrairu ya kaddamar da fara aikin tonon rijiyar Kolmani ta biyu a kusa da kauyen Barambu a Karamar Hukumar Alkaleri ta Jihar Bauchi.

An tona wannan rijiya ne zuwa zurfin mita 4,110, wanda idan aka lura akwai bambamcin mita dubu tsakaninsa da rijiya mafi zurfi da aka tona a baya a yankin.

A wannan rijiya ne aka tabbatar da samuwar mai a yankin Arewacin maso Gabashin Najeriya.

Kuma, wannan rijiya ta Kolmani ta 2, ita ta kawo karshen hasashe da kai ruwa rana da ake yi da wasu da ba su yarda cewa za a iya samun man fetur a Arewa maso Gabas ba.