Assalamu Alaikum Editan Aminiya a ba ni dama in yi tsokaci a kan amincewa da cigaba da neman man fetur a Arewa, musamman ma yankin mu na Arewa maso Gabas da qaramin Ministan man fetur na Najeriya ya sanar. Tabbas a matsayina na matashi, xan Arewa maso Gabas ina alfahari da wannan ci gaba da yankin mu zai samu a sakamakon wannan aiki da Gwamnatin talakawa ta Shugaba Muhammadu Buhari da ta yi mana, in har ya tabbata mun samu wannan mai. Ina kira ga ’yan uwana matasa da mu haxa kai mu bai wa gwamnatin tarayya da ma kamfanonin da su yi wannan aiki goyon bayan mu da ma haxin kai, domin wannan aiki ya yi nasara. Ina fata matasa kada mu bari wasu su yi amfani da mu, don yi wa wannan aiki qafar angulu, wanda muke fatan in har ya tabbata ya kawo sauyi a rayuwar al’ummar wannan yanki namu, wanda kusan mune koma baya ga dangi a cikin yankunan Najeriya. A qarshe ina fatan alkhairi ga Gwamnatin talakawa ta jam’iyan APC, wadda Shugaban qasa Muhammadu Buhari ke jagoranta. Allah ya qara hazaqa da hikima da basirar warware matsalolin Najeriya
Allah ka qara lafiya da nisan kwana ga Shugaba Buhari; Allah ka yi masa jagora wurin ciyar da qasa gaba.
Daga Ahmadu Manager Bauchi unguwar Karofin Madaki. 08065189242. [email protected].
Bashin tallafa wa manoma a Kebbi
Gaskiya bashin da Gwamnatin Muhammad Buhari ta qarqashin Babban Bankin Najeriya (CBN), ta bai wa manoman Jihar Kebbi, ya yi daidai, saboda hakan zai tallafa wa manoman jihar su yi noma yanda ya kamata, tunda an ba su kuxi da za su samar da dukkan kayan aiki da suke buqata, hakan zai sa su samar da wadataccen abinci a qasar nan, kamar yadda suka yi alqawari. Kuma abin da ya sa hakan yake da amfani, su manoman sun samu aikin yi, kuma abinci zai wadata a kasa, kuma gwamnati ma za ta samu kuxin shiga, kuma ya kamata gwamnatin tarayya ta tabbatar sauran jihohin ma am ba su, tunda a tsarin sun ce jihohi 13 ne za a bai wa rancen kuxin. Haqiqa idan jihohi 13 nan aka ba su wannan dama, to haqiqa abinci zai wadata a Najeriya, kuma rayuwa za ta yi sauqi. Muna roqon Allah ya sa wannan shiri na tallafa wa manoma ya yi nasara. Daga Muhammad Babangida Kiraji, Gashuwa. 08029388699. [email protected]
Ta’aziyyar Shugaba ’Yar’aduwa
Muna qara jajanta wa ‘yan uwa da iyalan marigayi tsohon Ahugaban Najeriya Malam Umar Musa Yar’adua, dangane da cikarsa shekaru shida da rasuwa da fatan Allah ya jiqan sa da rahama, ya kuma kyautata qarshen mu. Haqiqa mu Katsinawa ba za mu tava mantawa da Malam Umar Musa Yar’adua ba, saboda irin ayyukan alheri da ya gudanar a lokacin rayuwar sa. Domin haqiqa ya yi abin da ya dace matuqa. Fatan mu dai Allah ya sa ya huta.
Daga Comrade Sanin Shaga Kofar Kaura Katsina 08039433111 [email protected]
Fulani sun zama saniyar ware
Allah sarki Fulani, Fulani sun zama tamkar saniyar ware a qasar nan.’ Alal misali, in ka duba yadda a ke yi wa Fulani satar shanu ko kisan gilla, a sassa daban- daban, Kai ka ce su ba ’yan Najeriya ba ne. Da sun kai qara sai ya zama jami’an tsaro sun samu hanyar tatsar kuxi daga gare su, a qarshe ma sai rabin kuxin abin da ya vatan ya tafi a wajen cuku-cukun dawo wa da shi. Amma ya kasa dawowa. Daga qarshe a yi musu hanya-hanya. A zahirin gaskiya, ya kamata Gwamnatin Najeriya, da sauran jihohi, su samar da wani kwamiti da dai kawo qarshen kisan da a ke yi wa Fulani makiyaya, a samar musu da burtali, a qayyade su a waje guda. A tabbatar ba su shiga hurumin manoma ba. Ina ga in anyi haka za a samu sassaucin rigingimun manoma da makiyaya,.
Daga shugaban Muryar talaka reshen Ningi, Mudansir Ibrahim, Maishayi bakin Tasha Ningi, Bauchi Najeriya.
’Yan jarida ne jin mu da ganin mu
Ko shakka babu ‘yan jarida su ne jin mu da ganinmu. Amma sai dai Kash! Ba kowane xan jaridar ne ke aikinsa bisa alqawarin da ya xauka a lokacin rantsuwar kama aiki, ba. Haka a vangare xaya, da dama daga cikin hukumominmu a Najeriya, kan hana ‘yan jaridu damar yin aikinsu cikin ‘yanci. Tun daga rashin samun wadataccen bayani akan wani lamari, zuwa ga musgunawa wajen neman Labari.
Daga Abdulmalik Saidu Mai Biredi Tashar Bagu Gusau ( Jami’in Hulxa da Jami’a Na Qungiyar Muryar Talaka Reshen Jihar Zamfara) 08069807496 [email protected]
Haba qungiyar qwadago!
Assalamu alaikum. Haba qungiyar qwadago! Wane qarin albashi za a yi wa ma’aikata, bayan na farkon ma ba a biya ba? Har yanzu qarancin albashi yana nan kan N6000 a wasu qananan hukumomi na waxansu jahohi. Don haka mu ba wannan ya dame mu ba, kayan abinci da sauran ababen more rayuwa su daidata. Don shi ne mafi abin soyuwa ga al’umma, musamman daidai wannan lokaci da ’yan qasa suke halin ni ‘ya su. Allah dai ya kyauta; Ya taimaki shugabannin mu masu tausayin talaka amin.
Daga Nasiru Musa Maiyama Jihar Kebbi 08062206733/07066516731 [email protected]
Kira ga manyan Garo
Edita ka ba ni dama in roqi manya a cikin al’ummar mutanen Garo da ke Qaramar Hukumar Kabo, kan lallai su taimaka wajen ci gaban wannan qaramar hukuma ta mu. Domin na duba na ga cewa, idan har mutum ya taho tun daga Kanye zuwa cikin Kabo zai ci karo da ramuka da kwazazzabai, kai hatta a sauran sassan karkarar mu, waxanda suka haxa da Rugar Jawo da Vurawa da Kwankwamawa. Manyan Garo ku Allah Ya bai wa shugabanci, tun daga kan ’yan majalisar Jiha zuwa wakilanmu a majalissun tarayya, to ku taimaka wajen gyara yankunan karkarar mu, ko don matasa su daina kwarara birane neman abin da babu. Allah Ya sa ku tausaya wa al’ummar Qaramar Hukumar Kabo.
Daga Murtala Usher Kabo 08063445531.
Yabo ga Gwamna Masari
Yunqurin da Gwamnatin Jihar Katsina ke yi na inganta harkar ilimi abin a yaba ne matuqa. Tabbas wannan gwamnati qarqashin jagorancin Aminu Bello Masari ta duqufa wajen ganin harkar ilimi ta inganta. Muna godiya ga Dallatun Katsina.
Daga Mainasara Nasarawa Funtua. 08034208356 [email protected]
A karrama mutanen da ba su yi sata ba
Edita barka da qoqari,. Bayan haka ina mai amfani da wannan fili domin in roqi Gwamnatin Tarayyar Najeriya ta riqa fito da mutanen da suka riqe muqamai a matakai daban-daban a karrama su da kuma ba su lambar yabo, bisa la’akari da amanar da suka riqe ta qasa. Wannan tsari zai taimaka matuqa wajen assasa yaqi da cin hanci da satar dukiyar qasa, wanda jami’an gwamnati ke yi a matakai daban-daban na madafun iko, sannan hakan zai sanya a gano mutane da suka riqe amanar qasa kamar yadda Shugaban qasa Muhammadu Buhari yake ta qoqarin aiwatarwa a qasar nan . Bugu da qari, ina fata idan har za a riqa zaqulo ire-iren waxannan sahihan mutane, to wajibi ne a bi matakai na gwamnati uku, wato qananan hukumomi da jihohi da tarayya, domin kowa ya san cewa ana samun sahihan mutane masu riqe da amanar al’umma a kowane mataki na madafun iko a wannan qasa tamu. Daga [email protected] .