Shahararren dan kwallon Kamaru da yanzu haka yake bugawa kulob din Chelsea da ke Ingila, Samuel Eto’o a makon jiya ya ware zunzurutun Fam miliyan hudu, kwatankwacin Naira biliyan daya da dubu 55 inda ya sayo motocin garari hudu don jin dadin rayuwarsa.
dan kwallon, wanda ya taba lashe gwarzon dan kwallon Afirka har sau uku a jere ya ware zunzurutun Fam miliyan daya da dubu 55 kwatankwacin Naira miliyan 274 da dubu 300 wajen sayo mota kirar Bugatti beyron da tuni kamfanin ya gama kera ta kuma ya kai masa filin wasa na Chelsea mai suna Stamford Bridge da ke Ingila don gabatar da ita ga shi da sauran takwarorinsa.
Eto’o bai tsaya a nan ba, ya sake yin odar wata mota mai suna Aston Martin One-77 da aka kiyasta kudinta a kan Fam miliyan daya da dubu 25 kwatankwacin Naira miliyan 266 da dubu 500. Haka kuma dan kwallon ya sake sayar wata mota kirar Maybach denatec da aka kiyasta kudinta a kan Fam dubu 750 kwatankwacin Naira miliyan 195 sannna ya yi odar ta hudu kirar Aston Martin b12 Zagato a kan Fam dubu 450 kwatankwacin Naira miliyan 117.
dan kwallon ya bayyanawa kafofin watsa labarai a makon jiya cewa ya yi odar wadannan motoci ne don jin dadin rayuwarsa kuma yana fata hakan ba zai batawa wasu rai ba.
Samuel Eto’o ya sayi motocin garari hudu a kan Naira biliyan daya
Shahararren dan kwallon Kamaru da yanzu haka yake bugawa kulob din Chelsea da ke Ingila, Samuel Eto’o a makon jiya ya ware zunzurutun Fam miliyan…
