Idan muka dubi sana’ar DJ, wadda sana’a ce da duk lokacin da ake bikin aure, ake dauko matasa masu aiwatar da ita, inda suke kunna manya-manyan ganguna suna sanya wakoki matasa maza da mata na rawa, tare da nuna tsiraici da cudanya a tsakanin jinsin biyu. A irin wannan wuri shaidan kan taka muhimmiyar rawa wajen ganin cewa an sabi Allah.
Hakika duk wani Musulmin kirki mai tunanen sanadiyar halittarsa a doron duniyar nan, shi ne bautar Allah, tare da tunanen cewa zai hadu a ubangijinsa, ya kuma tambaye shi, duk wani abin da ya aikata a doron duniyar nan.
Ya zama dole, ya yi murna matuka da yunkurin Shugaban Qaramar Hukumar Gusau, na haramta Sana’ar DJ a duk fadin karamar hukumar mulkin Gusau.
Ganin yadda sana’ar take da matukar illa ga rayuwar matasa maza da matasa. Sanadiyar wannan sana’ar matasa da dama kan lalace, ganin yadda ake cudanya maza da mata wajen yinta. Kuma hakan kan haifar da zinace-zinace da bata tarbiyar matasa maza da mata.
Hanata zai taimaka wajen hana habbaka sabon Allah a doron kasa. Dan haka muna kira ga sauran Shugabannin Qananan Hukumomin Jihar Zamfara da su yi koyi da na Gusau.
Sai dai wani hanzari ba gudu ba, a da can baya babu wannan mummunar sana’ar.
Abin da muka sani shi ne; kidan kwarya, inda matan kan yi shi wasu-wasu sannu-sannu aka fara dauko masu kidan kwaryar a gidajen masu hannu da shuni.
Har aka wayi gari ana dauko mawaka suna sheke ayarsu (ga masu hannu da shunin kenan), yayin da masu dan karamin karfi kan samu DJ ya sanya musu wakokin da ke dauke da sauti mai dadi, mata da maza matasa na cashewa a kangon gida ko wani filin unguwa (saboda ko halin kama dakin taro babu).
Abin tambayar shin su wane ne masu DJ din?
Mene ya sanya su wannan sana’ar?
Wane tanadi aka yi wa masu, ganin an hana su sana’ar?
A zahiri dai ba mu ji an ba su wadannan matasan wani tallafi ko an koya musu wata sana’ar da za su rayu kanta ba, bayan sun bar DJ din.
SHAWARA!
Kamar yadda na fada a baya wallahi muna maraba da wannan yunkurin na Qaramar Hukumar mulkin Gusau.
To amma a fara yi wa tufkar hanci, ba wai sai mun kalli wata jahar ba, Jiharmu Zamfara ce, aka fara kafa shari’ar Musulunci. Kuma mun ga kokarin gwamnan farar hulla na farko (Sanata Ahmad Sani) ganin lokacin da ya yi kokarin tsayar da aikin assha! Ya yi kokarin sama wa masu aika-aikar wata madogara Wanda Alhamdulillahi! Duniya shaida ce, mafiya yawansu sun tuba kuma duniya shaida ce.
Don haka muna bai wa ita Qaramar Hukumar mulkin Gusau shawarar da ta bullo da wani shiri da zai hado kan matasan da ke wannan sana’ar tare da koyar da su wata sana’ar in sun kware a ba su tallafi domin su dogara da kansu.
Muddin aka yi haka Alhamdulillahi za a kawo karshen wannan matsalar cikin ruwan sanyi.
Sai dai idan aka ce haka kurum an hana matashi wajen da ya ke neman abinci, to wallahi an kamo hanyar da ba za ta bulle ba, domin dole ya nema wa kansa abinci ta kowane fanni. Ko ya Allah hanyar kwarai ko ta banza.
Haka zalika muna bai wa wannan karamar hukumar tamu shawara da ta hana gudanar da MUMMUNAR CACAR WASANNI TA ZAMANI da ake kira 9JA BET ko NAIRA BET Domin illarsu ta fi, ta sana’ar DJdin. Tunda wannan cacar tana haifar da sace-sace da lalaci iri-iri a cikin al’umma. Ko ba komai daukacin masu shagunan wannan cacar ba ainihin ‘yan Jihar Zamfara ba ne.
Bugu da kari muna kira ga mahukuntan da su tashi tsaye wajen yakar mummunar dabi’ar Shaye-shayen da ke fuskantar mu matasa ta hanyar yakar masu safarar kayan mayen zuwa Jihar Zamfara.
A karshe muna rokon Allah ya sa wannan koken namu zai karbu ga wadanda muka yi domin su.
Allah ka albarkaci matasan Jihar Zamfara da ma na Najeriya baki daya.
Tashar Bagu Gusau shi ne Jami’in Hulda da Jama’a na Qungiyar Muryar Talaka Ta kasa reshen Jihar Zamfara) 08069807496