✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Sama da mutum 400 sun rasu, 1,016 suka yi rauni a ambaliyar Tsunami a Indonesiya

Har yanzu ana ci gaba da gudanar da ayyukan ceto sakamakon mummunar annobar girgizar kasa da ambaliyar ruwa ta Tsunami da ta yi barna mai…

Har yanzu ana ci gaba da gudanar da ayyukan ceto sakamakon mummunar annobar girgizar kasa da ambaliyar ruwa ta Tsunami da ta yi barna mai tsanani a kasar Indonesiya.

Zuwa yanzu hukomomi a kasar sun tabbatar da mutuwar akalla mutum 281, yayin da wasu alkaluma suke cewa sun haura 400 sanidiyar annobar wadda ta auku a bayan girgizar kasa a gabar tekun Sunda na Indonesiya.

Kakakin Hukumar Bayar da Agaji da Magance Annoba ta Indonesiya (BNPB) Sutopo Purwo Nugroho ya ce sakamakon Tsunamin da ya biyo bayan girgizar kasar da ta auku gabar tekun Sunda da ke tsakanin Tsibiran Sumatra da Jaba adadin wadanda suka mutu sun kai 281 inda wadansu 1,016 suka samu raunuka kamar yadda kafar labarai ta TRT ta ruwaito.

Nugroho ya ce, wadansu karin mutum 57 sun jikkata sakamakon Tsunamin, inda ya yi gargadin yiwuwar sake aukuwar Tsunami a yankin wanda dutse mai aman wuta na Anak Krakatau yake yi wa barazana saboda wuta da hayakin da yake fitarwa.

Nugroho ya kara da cewa a fadin yankin da lamarin ya faru an sace kayan bayar da gargadi kan yiwuwar aukuwar Tsunami ko kuma sun lalace inda tun daga shekarar 2012 ake fuskantar matsalar gargadi a yankin.

A gefe guda, bayanan da aka yada a shafukan sada zumunta cewa sakamakon sace kayan bayar da gargadi kan yiwuwar aukuwar Tsunami ne ya jawo asarar rayukan kuma jami’an gwamnati ne ke da alhakin mutuwar al’umma, inda hukomomi suka ce aman wuta da dutsen Anak Krakatau ya yi ne musabbabin lamarin.

A ranar 28 ga Satumba a gabar tekun Palu da ke Tsibirin Sulawesi girgizar kasa mai karfin awo 7.5 ta auku inda daga baya Tsunami ta faru tare da kashe mutane sannan sama da 1,500 suka bata da har yau ba a gan su ba.