✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Sama da mutum 20 ke kokarin maye gurbin marigayi Wakili

Biyo bayan mutuwar Sanata Ali Wakili na jam’iyyar APC mai wakiltar yankin Bauchi ta Kudu mako biyu da suka gabata akwai alamun kokarin da wasu…

Biyo bayan mutuwar Sanata Ali Wakili na jam’iyyar APC mai wakiltar yankin Bauchi ta Kudu mako biyu da suka gabata akwai alamun kokarin da wasu ke yi don maye gurbinsa kamar yadda dokar zabe ta tanada cewa duk wani dan majalisa da ya rasu a maye gurbinsa cikin kwanaki 90.
 
Wakili wanda ya rasu a ranar 17 ga watan Mayu, an binne shi ne a Abuja kuma an yi jana’izarsa a gidansa da ke Bauchi inda dubban mutane suka rika yin tururuwa gidansa don jajantawa iyalinsa.
 
A yanzu dai fiye da mutum 20 ne ke kokarin  tsayawa takara don maye gurbinsa a zaben da za a gudanar.