✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Sam Buhari bai fahimci zanen gadar da Ganduje ya kai masa ba – Kwankwaso

A farkon makon nan ne dai Ganduje ya kai zanen wata gadar sama mai hawa uku ga Buhari a Fadar Shugaban Kasa dake Abuja

Tsohon Gwamnan jihar Kano, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso ya ce sam Shugaban Kasa Muhammadu Buhari bai fahimci zanen gadar da Gwamna Abdullahi Ganduje ya kai masa ba.

A farkon makon nan ne dai Ganduje ya kai zanen wata gadar sama mai hawa uku ga Buhari a Fadar Shugaban Kasa dake Abuja wacce ya kudiri aniyar ginawa a kan shatale-talen NNPC dake unguwar Hotor a birnin Kano.

Sai dai a wata tattaunawarsa da Sashen Hausa na BBC ranar Juma’a, Sanata Kwankwaso ya ce yana matukar mamakin yadda Gandujen ya ciyo bashin Naira biliyan 20 da nufin yin aikin da ya ce na Gwamnatin Tarayya ne.

Ya kuma zargi Gwamnan da gaza fahimtar hakikanin bukatar jama’ar jihar Kano, inda ya ce kamata ya yi harkar ilimi ta kasance a kan gaba ba wai gina gadar sama ba.

“A maimakon Ganduje da ya je ya ga Shugaban Kasa ya roke shi ya yi aikin gadar, saboda aikin Gwamnatin Tarayya ne yin gadojin sama a kan hanyar Kano zuwa Wudil, amma sai ya je ya bige da nuna wa mishi hoton da ba a zana shi yadda ya kamata ba, wanda kuma hatta shi Buharin ma bai fahimta ba. Akwai abinda ya fi wannan a Ofishin Shugaban Kasa,” inji Kwankwaso.